Ana tsare da Aung San Suu Kyi a gida bayan zaman kurkuku da ta yi a birnin Naypyitaw. Tana tsare tun ne lokacin da sojoji suka kwace mulki a farkon shekarar 2021./ Ann Wang/Reuters

Shugabar farar-hular kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, wacce ke tsare tun bayan hambarar da ita a juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2021, tana daga cikin fursunoni dubu 7 da gwamnatin soji ta yi wa afuwa albarkacin hutun azumin Bhuddist na kasar.

"Za a rage mata zaman gidan yari na shekaru shida," a cewar kakakin gwamnatin mulkin soji Myanmar Zaw Min a yayin hira da manema labarai a ranar Talata.

Ya kara da cewa an yi Suu Kyi afuwa ce kan laifuka biyar cikin laifuka 19 da ake tuhumarta da aikatawa.

Ana tsare da Aung San Suu Kyi, wacce ta lashe kyautar Nobel, a gida bayan zaman kurkuku da ta yi a birnin Naypyitaw. Tana tsare ne tun bayan da sojoji suka kwace mulki daga hannunta a wani juyin mulki da aka yi a farkon shekarar 2021

A ranar Talata ne gidan rediyo da talabijin na Myanmar ya ba da rahoton afuwar da shugaban majalisar gudanarwar gwamnatin kasar ya yi mata amma wata majiya mai tushe ta ce za a ci gaba da tsare Suu Kyi.

"Ba za ta samu 'yanci daga tsare ta da ake yi a gida ba," in ji majiyar da ta ki amincewa a ambace ta saboda dalilai na tsaro.

Suu Kyi, mai shekaru 78, ta yi gwagwarmayar samar wa kasarta ‘yancin kai, kuma an fara tsare ta ne a gidanta a shekarar 1989 bayan wata gagarumar zanga-zangar adawa da mulkin soji da aka kwashe shekaru da dama ana yi a Myanmar.

A shekarar 1991, ta samu lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya don fafutukar tabbatar da dimokuradiyya.

Ta lashe zaben 2015, wanda aka gudanar a matsayin wani bangare na shirin mika mulki daga hannun soji zuwa farar-hula da aka kawo karshensa a juyin mulkin 2021.

Ta daukaka kara kan laifuka daban-daban da suka hada da tunzura jama’a da zamba da kuma cin hanci da rashawa. Ta musanta dukkan tuhumar da ake mata.

TRT World