Har yanzu ba a san karin yawan wadanda suka mutu a garin da ke can cikin surkuki ba a yankin Sagaing /Hoto: AP

Sojojin juyin mulki da ke mulki a Myanmar sun tabbatar da cewa sun kai harin sama a kan wani kauye inda rahotanni suka ce ya hallaka mutum 100, lamarin da ya jawo suka daga Majalisar Dinkin Duniya da shugabannin Yammacin Duniya.

Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta MDD Volker Turk ya ce "ya tsorata kwarai" da mummunan harin saman, wanda cikin wadanda suka mutu har da yara 'yan makaranta da suke raye-raye.

Hukumar ta bukaci lallai a gurfanar da wadanda suka aikata hakan a gaban kuliya.

Har yanzu ba a san karin yawan wadanda suka mutu a garin da ke can cikin surkuki ba a yankin Sagaing.

Rahotannin farko-farko sun ce mutum 50 ne suka mutu, amma daga baya kafafen yada labarai masu zaman kansu na kasar sun ce yawan ya kai 100.

Zai yi wahala kwarai a iya tabbatar da cikakkun bayanai kan harin saboda gwamnatin sojin ta hana duk wata hanya ta samun rahoto.

Sashen BBC Burma da Irrawaddy and Radio Free Asia da kuma ganau din da kamfanin dillancin labarai na AFP suka zanta da su sun ruwaito cewa a kalla mutum 50 ne suka mutu yayin da gommai suka jikkata.

A ranar Talata da daddare gwamnatin sojin ta tabbatar da batun kai harin saman, amma ba ta fadi yawan mutanen da suka mutu ba.

Mai magana da yawun gwamnatin Zaw Min Tun, ya ce "An yi wani taro na bikin kaddamar da wata runduna wai ita People's Defence Force... (Talata) da safe wajen karfe 8 a kauyen Pazi Gyi," yana magana a kan kungiyoyin dakarun juyin mulki da suka yadu a kasar tun bayan hambarar da gwamnatin dimokradiyya a juyin mulkin da aka yi a 2021. "Mun kai hari wajen."

Daga cikin wadanda suka mutu har da mayakan da ke adawa da juyin-mulki da ke sanye da kaki, duk da cewa "akwai yiwuwar har da fararen hula".

Sai dai mai magana da yawun gwamnatin ya kuma dora laifin a kan rundunar People's Defence Force din da dasa nakiyoyi da suka yi sanadin jawo mace-macen.

'Bam aka jefa a kan taron mutane'

Wani mutum da ke da alaka da rundunar People's Defence Force da ya ceci mutane a wajen ya shaida wa AFP cewa mata da yara na daga cikin wadanda suka mutu.

Bayan gano gawarwaki da kuma kai wadanda suka jikkata asibiti, ya kiyasta cewa wadanda suka mutu za su kai 100 ko ma su fi.

"Ina tsaye a dan nesa da inda cincirindon mutane suke a lokacin da wani abokina ya kira ni a waya ya shaida min cewa jirgin yaki yana tahowa ta wajen," in ji ganau din.

"Kai tsaye jirgin yakin ya jefa bam a kan taron jam'ar, nan da nan na yi tsalle na fada cikin wani rami da ke kusa na buya. Jim kadan bayan hakan, da na mike tsaye na kalli wajen, sai na ga gawarwakin mutane birjik suna cin wuta.

"Wuta ta lalata ginin wajen. Kusan mutum 30 sun jikkata. A yayin da ake kwashe mutane don kai su asibiti kuma sai ga wani helikwafta ya iso ya sake harbe wadansu mutanen. A yanzu muna ta kona gawarwakin da gaggawa. "

Ya ce kusan mutum 150 ne suka taru don halartar bikin kuma kusan mata 20 da yara 30 na daga cikin wadanda suka mutun, yana mai cewa cikin mamatan har da shugabannin kungiyoyin da ke adawa da gwamnati a yankin da sauran kungiyoyin hamayya.

Duk da cewa MDD ba ta tabbatar da yawan wadanda suka mutun ba, Mista Turk ya zargi gwamnatin sojin Myanmar da "gaza kare rayukan fararen hula."

TRT World