An shirya tsaf don harba tauraron ɗan'adam na sadarwa ƙirar Turkiyya na farko zuwa samaniya a watan Yuli.
Ranar Laraba ne aka yi jigilar kumbon tauraron Turksat 6A zuwa tashar harba kumbo ta Cape Canaveral Spaceport a Florida, Amurka, don harba shi zuwa samaniya. Jirgin da ya kai kumbon tauraron ya yi tafiyar awanni 19 daga filin tashin jirgi na Murted Airspace Command da ke Ankara.
Kumbon tauraron, wanda aka kai sansanin SpaceX bayan shirye-shirye da suka ɗauki tsawon awanni huɗu, an shirya harba shi zuwa samaniya cikin makon ranar 8-15 na watan Yuli, daidai da yadda yanayi ya ba da dama.
Injiniyoyin Turkiyya ne suka ƙera tauraron ɗan'adam na Turksat 6A a Ma'aikatar Fasahar Sararin Samaniya ta Turkish Aerospace Industries, tare da tallafin Ma'aikatar Sufuri da cigaban ƙasa, Tubitak Uzay, Aselsan da C2TECH.
Tauraron shi ne na farko cikin shirin da babbar cibiyar bincike da cigaban ƙasa ta Turkiyya.
A yanzu kamfanin Turksat yana sarrafa tauraron ɗan'adam na sadarwa guda biyar, wato Turksat 3A, 4A, 4B, 5A da 5B, kan digiri 31, da 42 da 50 a falakin gabashi, wanda ke isa ga jimillar mutane biliyan 3.5.
Bayan ƙaddamar da tauraron Turksat 6A, faɗin da za a iya kamowa daga Turkiyya zai kai har zuwa Indiya, Thailand, Malaysia da Indonesiya, wanda ke nufin ƙarin iso zuwa mutane sama da biliyan biyar a faɗin duniya, inda ya kai kashi 65 cikin 100 na al'ummar duniya.