A baya kamfanin ya taba gwada makami mai linzamin a watan Oktoban 2022 /Hoto: OTHERS

Kamfanin kera makamai masu linzami na Turkiyya, Roketsan, ya yi nasarar gwajin harba makami mai linzami mai tafiyar gajeren zango na Tayfun (Typhoon) a Bahar Aswad da ke yankin Rize a kasar.

An gudanar da gwajin makamin Tayfun ranar Talata da misalin karfe 6.44 na yamma agogon kasar wato daidai da 3.44 na yamma agogon GMT.

Ismail Demir, shugaban Hukumar Masana'antun Tsaron Turkiyya, ya taya dukkan 'yan tawagar da suka yi aikin murna.

"Mun yi nasarar gudanar da sabon gwajin makami mai linzaminmu na Typhoon. Ina taya dukkan wadanda suke da hannu wajen tabbatuwar hakan, musamman ma kamfanin Roketsan," a cewar Demir.

Zuwa yanzu dai Tayfun shi ne makami mai linzami mafi tafiyar dogon zango da Turkiyya ke da shi.

A baya kamfanin ya taba gwada makami mai linzamin a watan Oktoban 2022, a lokacin da ya kai wani zango mai nisan kilomita 560.

TRT World