Turkiyya ta lallasa Georgia da ci 3-1 a Gasar Euro 2024 a karawar da suka yi a ranar Talata.
Mert Muldur ne ya sa Turkiyya ta shiga gaba da ci ɗaya tun kafin hutun rabin lokaci bayan ya zura wa Georgia ɗin kwallo a raga.
Georgia, wanda wannan ne karo na farko da take buga wata babbar gasa ta ƙasa da ƙasa, ta rama ci ɗaya wanda ya ja suka yi kunnen doki a minti na 32 da soma wasan a lokacin da Giorgi Kochorashvili ya yi kurosin sannan Georges Mikautadze ya zura ta a raga.
A minti na 65 Guler ɗan shekara 19 wanda ke buga wa Madrid wasa ya ci wa Turkiyya ƙwallo ta biyu.
Georgia ta yi ta ƙoƙarin rama ci na biyun da aka yi mata inda ta yi ta ƙoƙarin bugun kusurwa, sai dai ta yi rashin sa’a inda Kerem Akturkoglu na Turkiyya ya ɓalle sannan ya zura ƙwallo ta uku a cikin ragar Georgia.
A lokacin da ya zura ƙwallon, golan Georgia ba ya gida sakamakon ya tafi taya sauran ‘yan wasan ƙasarsa neman cin Turkiyya ƙwallo ta biyu a lokacin da ake bugun kusurwa.
Wasa na gaba da Turkiyya za ta buga za ta kara ne da Portugal da Jamhuriyar Czech. Idan Turkiyya ta kammala wasan rukuni da maki mai kyau, za ta tafi wasan zagayen ‘yan 16.