An kama wata mamba ta ƙungiyar ta'addanci ta PKK/KCK, reshen mata a ƙasar Norway, Sirin Tokpinar, a birnin Istanbul.
An yi nasarar kama ta a ranar Laraba ne sakamakon aikin hadin gwiwa na Hukumar Leƙen Asiri ta Turkiyya MIT da kuma Sashen Tsaro na Yankin Istanbul.
An kama Tokpinar ne bayan wani aiki da aka gudanar cike da taka tsantsan a Turkiyya, bayan gano cewa ta shiga ƙasar.
Tokpinar tana taka rawa sosai a al'amuran PKK/KCK a Turai, musamman ma a ƙasar Norway.
Sannan kuma da hannunta a duk wata harka ta musayar kuɗaɗe a madadin ƙungiyar ta'addancin.
A cikin fiye da shekara 35 da ta shafe tana yaƙi da Turkiyya, ƙungiyar PKK - wacce Amurka da Tarayyar Turai da Turkiyya suka ayyana a matsayin ta ta'addanci - ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40,000 da suka haɗa da mata da yara da jarirai.