Turkiyya ta kai smaame kan wata ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta masu aikata miyagun laifuka ta Comanchero, inda aka kama mutum 37 da ake zargi a Istanbul, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya.
An tarwatsa ƙungiyar Comanchero, wacce ke da cibiya a Australia da Hakan Ayik (REIS) ke jagoranta, take kuma ayyukanta a faɗin duniya, a yayin samamen da aka kai a Istanbul, akamar yadda Ali Yerlikaya ya faɗa a ranar Alhamis.
Yerlikaya ya ƙara da cewa an kama mutum 37 da ake zargi a yayin samamen.
“Ba za mu yafe wa duk wani gungun masu aikata miyagun laifuka ba, masu safarar ƙwaya. Za mu tarwatsa su duk irin ƙarfinsu tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya," in ji ministan.
Da yake ƙarin bayani a kan ƙungiyar, Yerlikaya ya bayyana cewa an kashe ainihin shugaban ƙungiyar miyagun laifukan a shekarar 2018.
Ƙungiyar ta ci gaba da munanan ayyukanta a fadin duniya ƙarƙashin jagorancin Mark Douglas Buddle, ciki har da safarar miyagun ƙayoyi da kisan kai da fashi da makai da satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
A shekarar 2022 an kama Buddle a Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya sannan aka mayar da shi Australiya.
Hakan Ayik da Duax Hohepa Ngakuru, biyu daga cikin mambobin ƙungiyar sun karɓi jagorancinta tare da ci gaba da aiwatar da munanan ayyukan.