Mutane na ziyartar hubbaren Mustafa Kemal Ataturk da ke Ankara/ Hoto: Reuters

Mustafa Kemal Ataturk, wanda shi ne ya kafa Jamhuriyar Turkiyya kuma shugaban kasar, ya shiga tarihi ba wai kawai a matsayin kwamandan da ya yi nasarar jagorantar yaƙin neman ‘yancin kai na kasar Turkiyya ba, har ma a matsayinsa na mai fada a ji da juyin juya hali.

Kamar yadda yake a al'ada duk ranar 10 ga watan Nuwamba a Turkiyya, ana tsayar da al'amuran yau da kullum cak da misalin ƙarfe 9.05 na safe, inda ake kunna ƙarar jiniya da za ta karaɗe kowane lungu da saƙo na ƙasar, don tunawa da daidai lokacin da Ataturk ya mutu yana da shekara 57, inda miliyoyin mutane a faɗin ƙasar ke yin jimami ta hanyar yin tsit na minti biyu.

A ginin Anitkabir da kushewar Ataturk take wanda ke babban birnin ƙasar Ankara, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya jagoranci wani taron tunawa da kuma girmama jagoran na Turkiyya.

"Ya mai girma Ataturk, a tunawa da cika shekaru 85 da rasuwarka, muna sake tunawa da jajircewarka da mutuntakarka mai girma, da dakarunka masu sadaukarwa, da jarumtakar shahidan da suka rasa rayukansu saboda al'ummarmu, da kuma tsofaffin sojojin da suka zubar da jininsu bisa manufa ɗaya," ya rubuta a cikin littafin tunawa.

Shugaba Erdogan ya ajje fure a hubbaren Ataturk, sannan ya yi shiru na dan lokaci, sai kuma ya rera taken kasa tare da sauran jagoriri.

An haifi Ataturk a shekarar 1881 a garin Thessaloniki na kasar Girka, wanda a wancan lokacin yana karkashin Daular Usmaniyya, iyayensa su ne Ali Riza Efendi da Zubeyde Hanim. Mahaifinsa ya rasu a lokacin da Ataturk ke ƙarami.

Ya fara karatu a kwalejin sojoji a 1893 a garin Thessaloniki. A wannan makaranta da ya samu kwarewar soji, Ataturk ya kuma koyi yaren Faransanci.

Ya ci gaba da karatunsa a makarantar sojoji da ke Istanbul inda ya kammala a matsayin Laftanal a 1902.

Tare da irin hikima da ƙwarewar da yake da su, nan da nan sai Ataturk ya dinga samun matsayin soji inda ya samu muƙamin 'staff captain' a 1905.

Jama'ar Turkiyya a fadin kasar na yin tsaiwa ta mintuna biyu don girmamawa ga shugaban kasa na farko a jumhuriya, wadda a watan da ya gabata ta cika shekaru 100 da kafuwa.

Shekarar 1911 ta zama mai muhimmanci a rayuwar Ataturk inda a wannan lokacin ne ya yaƙi Italiyawa a Tarabulus har ya samu babbar nasara, wacce ta tabbatar da ƙwarewarsa a ayyukan soji.

Ya ja hankalin mabiyansa da irin ayyukansa, bayan fara yakin balkan a 1912. A lokacin da yake mukamin manjo, ya taka babbar rawa wajen kwato lardunan Dimetoka da Edirne.

A 1914 lokacin da Ataturk na wakiltar sojin Turkiyya a Sophia, sai aka fara yakin duniya na farko, kuma kawancen kasashe suka jibge dakarunsu a yankin gabar teku na Gallipoli inda aka fara gangamin Dardanelles.

A wata wasiƙa da ya aika ga mukaddashin kwamanda Envar Pasa, Ataturk ya bukaci da ya fita filin daga inda ya dakatar da ayyukansa na Sophia.

Da misalin karfe 9.05 (0605GMT), an i karar jiniya a fadin kasar don tuna lokacin da ran Ataturk ya fita yana da shekaru 57. Hoto: AA

Ataturk da sojojin Turkiyya sun kafa tarihi wajen nuna tirjiya. Umarnin Ataturk ga sojojinsa a wajen yakin na ci gaba da motsawa a zukatan Turkawa: "Ba ina umartar ku da ku kai hari ba ne. Ina umartar ku da ku mutu ne."

Tauraruwarsa ta ci gaba da haskawa a yayin ayyukansa a arewa maso-yammacin Edirne da kudu maso-gabashin Diyarbakir a 1916, wanda hakan ya samar masa da matsayin manjo janar a wannan shekara.

Ya yaki sojojin Ingila a Sham a 1918, sanna ya jagoranci tirjiyar bijire musu.

Bayan da ƙawancen kasashen Yamma suka mamaye Istanbul a 1919, Ataturk ya je garin Samsun na arewaci a matsayin supetan sojo na tara, wanda a nan ne ya sauya rayuwarsa da ta Turkiyya baki daya.

Jama'a a Istanbul sun taru a Fadar Dolmabahce, wajen da Ataturk ya mutu shekaru 85 da suka gabata.

Bayan ya bayyana cewar za a iya kubutarwa da 'yantar da kasarsu ne daga mamayar 'yan kama guri zauna idan har al'umma na so, ya shirya manyan taruka biyu a garuruwan Sivas da Erzurum, inda aka tattauna kan yaƙin ƙwatar 'yancin kasar.

A ranar 23 ga Afrilu 1920, an kafa Babbar Majalisar Dokokin Turkiyya, kuma an zabi Ataturk a matsayin shugaban gwamnati kuma kakakin majalisa, wanda ya ba shi damar samar da dokokin da za su fatattaki 'yan kama guri zaunar.

A ranar 15 ga Mayun 1919 aka fara gwagwarmayar neman 'yancin Turkiyya, a lokacin da Hasan tahsin ya harba harsashi na farko kan 'yan mamaya na sojojin Girka, an kashe sojan Turkiyya daya bayan wannan abu.

A fadin kasar, mutane suna tsaya wa a kan tituna ko su tsyaa cak a wuraren ayyukansu su yi shiru don tuna Ataturk.

Dakarun sojin Turkiyya, karkashin shugabancin Ataturk sun samu gagarumar nasara kan dakarun 'yan mamaya - da kuma yake-yaken Inonu na farko da na biyu, Sakarya da Babban Farmaki - har zuwa 1923 lokacin da aka sanya hannu kan Yarjejeniyar Lausanne a ranar 24 ga Yuli.

Nasarar da aka samu a filin daga ce ta kai ga ayyana Jumhuriyar Turkiyya a ranar 29 ga Oktoba 1923.

Ataturk ya zama shugaban kasa na farko na jumhuriyar Turkiyya har zuwa 10 ga Nuwamba 1938, lokacin da ya rasu a Istanbul yana da shekaru 57.

Ana tunawa da Ataturk ta hanyar buki a dakinsa da ke Fadar Dolbahce da ya mutu a cikin sa. Bayan bukin tunawar, ana bude wa jama'a dakin don ziyara.
AA