Turkiyya na sake nazarin matakanta na tsaro don kare na'urorin sadarwa da sojojinta suke amfani da su, bayan mummunar farfashewar na'urorin sadarwa da aka samu a Labanon, kamar yadda wani jami'i na ma'aikatar tsaron Turkiyya ya bayyana ranar Alhamis.
A ranar Laraba ne na'urorin sadarwa na hannu na Hizbullah suka ringa fashewa a kudancin birin Lebanon, wacce ta zama rana mafi muni a ƙasar tun bayan ɓarkewar yaƙin kan iyaka tsakanin ƙungiyar Hizbullah da sojojin Isra'ila kusan tsawon shekara guda, abin da ya tayar da hankula bayan irin wannan farfashewar da aka fuskanta a na'urorin sadarwa na pager na Hizbullah ranar Talata.
Fashewar ta jefa ruɗani ga Hizbullah, wacce ita ce babbar ƙawar Iran da take yi mata yaƙin bayan fage a Gabas ta Tsakiya, kuma ta faru ne a daidail lokacin da kisan da Isra'ila ke yi wa Falasɗinawa a Gaza ya shiga wata na 11 da kuma ƙaruwar fargabar fantasamar yaƙin zuwa wasu sassan nahiyar.
Jami'in na Turkiyya ya ce Sojojin Turkiyya suna amfani ne kawai da na'urorin da aka ƙera a cikin ƙasa, amma hukumomi a Ankara na ɗaukar ƙarin matakai idan wani daga waje ya shiga harkar sayowa ko kuma ƙera na'urorin.
"A duk ayyukan da muke yi, ko yaƙin da ake yi yanzu haka a Ukranine, da kuma Alala misali Labanan, ana sake nazarin matakan ana kuma fito da wasu sababbin matakan a matsayin wani darasi da aka koya, sakamakon yadda abubuwa suke sauyawa," a cewar jami'in.
"Duba da abin nan da ya faru, mu a matsayinmu na Ma'aikatar Tsaro muna yin duka binciken da suka kamata a yi," a cewar mutumin, ba tare yin ƙarin bayani ba.
A fashewar da aka samu a ranar Talata, wasu majiyoyi sun ce, daga nesa jami'an leƙen Isra'ila suka tayar da abubuwan fashewa da aka makala a cikin na'urorin sadarwa 5,000 da Hizbullah ta yi odarsu, waɗanda kuma an maƙala su ne kafin a shigar da su ƙasar.
Harin da ba a taɓa ganin irinsa ba ya sa ana bayyana damuwa kan tsaron harkokin sadarwa a yankin.
A ranar Laraba, majalisar tsaron Iraki ta ce za ta ɗauki matakan riga-kafi kan yiwuwar yin kutse daga kayan latironi da aka shiga da su ƙasar, tana mai ƙarawa da cewar za a ringa tsaurara binciken tsaro kan kayan da ake shigar da su, tare da zuzzurfan bincike a kan iyaka.
A ranar Alhamis, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya shaida wa kamfanin dillacin Labarai na Anadolu cewa, kafa wata cibiya mai zamna kanta musamman kan tsaron intanet yana daga cikin abin da gwamnati ta sa a gaba, bayan Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana wajibcin hakan, sannan ya ƙara da cewa za a kafa ta "nan da ba jimawa ba."