Mamayar kasashen waje a karshen yakin duniya na ɗaya ne ya zaburar da yakin 'yancin kai na Turkiyya a shekarar 1919, inda sojojin Turkiyya karkashin jagorancin Ataturk suka fatattaki mahara daga yankin Anatoliya. / Hoto: AA  

Turkiyya na bikin tunawa da Ranar Nasara karo na 102, domin karrama gagarumar nasarar da aka samu kan sojojin Girka da suka mamaye yankin Dumlupinar a shekara ta 1922.

Yaƙin dai wani ɓangare ne na farmakin da sojojin Turkiyya suka ƙaddamar a ranar 26 ga watan Agustan shekarar 1922 ƙarƙashin jagorancin shugaban da ya kafa jamhuriyar Turkiyya Mustafa Kemal Ataturk, kana aka kawo ƙarshensa a ranar 18 ga watan Satumban shekarar.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan da manyan jami'an gwamnati da na sojojin ƙasar sun ajiye furanni a Anitkabir, maƙabartar da aka binne Ataturk a Ankara babban birnin ƙasar.

A wannan muhimmiyar rana, ɗaya daga cikin muhimman abubuwa a tarihinmu, ina taya mu muryar ranar nasara ta 30 ga watan Agusta a ƙasarmu abar alfaharinmu,'' in ji Erdogan.

A yayin da yake miƙa sakon taya murna ga al'ummar Turkiyya a faɗin duniya, Shugaba Erdogan ya jaddada cewa, a yaƙin da aka yi a ranar 30 ga watan Agusta, an samu gagarumin nasara a kan sojojin da suka yi mamaya, sannan aka tarwatsa tsarin mulkin mallaka kana aka buɗe ƙoƙofin kafa jamhuriya.''

Erdogan ya kuma jaddada cewa, da wannan babbar nasara wadda Ataturk ya bayyana a matsayin ''muhimmin tarihi mara gushewa a rayuwar al'ummar Turkiyya na samun 'yanci da dogaro da kai," Turkiyya ta shaida wa duniya baki ɗaya cewa ''ba za ta bari a ɗaure ta ba kuma ba za ta taɓa bari a take haƙƙinta na zama ƙasa mai cikakken iko ba.''

Shugaban ya kuma jaddada aniyar Turkiyya ta taimakon al'ummar da ake zalunta a faɗin duniya, yana mai cewa: "Muna haɗa ƙarfi da ƙarfe domin kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da zalunci da kuma kisan kiyashi da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya, musamman a Gaza."

Al'ummar lardin Mugla da ke kudancin Turkiyya, sun gudanar da bukukuwan murnar zagayowar ranar nasara, tare da raye-raye a bayyanar jama'a.

Kawo ƙarshen mamaya

Dakarun Ƙawance sun yi wa Turkiyya mamaya ne bayan samun galaba kan Daular Usmaniyya a ƙarshen Yaƙin Duniya na Ɗaya a shekarar (1914 zuwa1918).

Waɗanda suka yi nasara a yaƙin, waɗanda ake ce musu Ƙasashen Ƙawance ko kuma 'Entente Powers,' a Turance sun sauka a Turkiyya ta yanzu a shekarar 1919, inda suka mamaye yankin mai yawa kamar yadda Yarjejeniyar Mudros ta tanada.

Mamayar ƙasashen waje ya zaburar da yakin 'yancin kai na Turkiyya a 1919, inda sojojin Turkiyya - ƙarƙashin jagorancin Ataturk - suka fatattaki mahara daga yankin Anatoliya.

An yi ta shawagi da balan-balan iska mai zafi a yankin Cappadociaya a sararin samaniya ɗauke da tutocin Turkiyya domin nuna murnar gagarumar Nasara da kasar ta samu.

Daga ranar 26 zuwa 30 ga watan Agustan shekarar 1922 sojojin Turkiyya suka fafata a yakin Dumlupinar (wanda ake la'akari da yakin Girka da Turkiyya ) a lardin Kutahya da ke yammacin kasar Turkiyya, inda aka samu galaba a kan sojojin Girka.

A ƙarshen shekarar 1922, sojojin ƙasashen waje baki ɗaya sun bar yankunan waɗanda suka zama sabuwar Jamhuriyar Turkiyya bayan shekara ɗaya.

TRT World