Kasashen Turkiyya da Italiya sun samu damar karbar bakuncin Gasar Cin Kofin Kasashen nahiyar Turai (EURO) a shekarar 2032, yayin da kasashen Birtaniya da Ireland su ne za su karbi bakuncin gasar a 2028, kamar yadda hukumar kula da harkokin kwallon kafa a Turai UEFA ta bayyana.
Kasashen Turkiyya da Italiya sun samu damar karbar bakuncin Gasar Cin Kofin Kasashen nahiyar Turai (EURO) a shekarar 2032, yayin da kasashen Birtaniya da Ireland su ne za su karbi bakuncin gasar a 2028, kamar yadda Hukumar Kula da Harkokin Kwallon kafa a Turai (UEFA) ta bayyana.
An sanar da hakan ne yayin wani biki a ranar Talata bayan wani taron Kwamitin Zartarwa na UEFA a birnin Nyon.
"An gabatar da filayen wasa 20 da ake son a yi amfani da su wajen karbar bakuncin wasa, 10 daga ciki ne za a zaba, biyar da kowace kasa, zuwa watan Oktoban shekarar 2026," in ji Hukumar UEFA.
Birtaniya da Ireland sun gabatar da filayen wasanni da dama ciki har da na Belfast da na Birmingham da na Cardiff da na Dublin da na Glasgow da na Liverpool da na London da na Manchester da na Newcastle
Wannan ne karon farko da Turkiyya take karbar bakuncin Babbar Gasar nahiyar Turai, yayin da wannan ne karo na uku da kasar Italiya take karbar bakuncin.