Santambul, wani tsohon birni ne da ya ratsa nahiyoyi biyu kuma a tsawon shekaru, ya yi fice a wakoki iri daban-daban masu shiga rai da karfafa gwiwa da zane-zane da kuma litattafai.
Wata kungiya mai zaman kanta a Turkiyya, wacce ke kula da lafiyar kwakwalwa ta gudanar da wani bincike kan yadda mutane ke ji game da wasu wurare a Santambul.
An kirkiri taswirar yadda mutane ke ji don taimaka musu yin zabi kan wajen da za su iya zuwa la’akari da yanayinsu.
Hasumiyar soyayya ta 'Maiden’s Tower'
Ginin Hasumiyar Maiden's Tower, yana kan wani karamin tsibiri a mashigin Santambul ta teku, ana daukarsa a matsayin wurin soyayya mafi girma a birnin.
Alamarsa na nuni kauna da soyayya mara iyaka, in da hasumiyar mai ban sha'awa ke jan hankalin baki masu son yin soyayya a wurin mai ban sha'awa da kyau da ya ratsa mashigin birnin na Istanbul.
Wurin da aka aza hasumiyar na kan tsibirin teku, yanayin da ake ganin yana kara dankon soyayya, sannan dangantakar da wajen ke da shi na tarihi ya kara masa matsayi.
Muhimmancinsa ya dada girma ta hanyar tattara fahimta da ma’anar da mutane ke yi wa wajen.
Zeynep Ahunbay, Farfesa kan Fasahar Gine-Gine a Jami'ar Fasaha ta Istanbul ta yi bayanin cewa nisan hasumiyar na kara mata kyau da ban sha'awa.
"Idan kuma ka kalle ta daga nesa, sai ku ga kamar tana tsaye a wajen da ba za a iya isa ba, sai hakan ke bayar da sha'awa. Fasalin gininta da babu irinsa na kara mata kyau da kwarjini.
Hasumiyar na da muhimmanci sosai tun tale-tale, amma tsawon lokaci, sai ta zama mai bayar da ma'anoni daban-daban," in ji Ahunbay, yayin tattaunawrsa da TRT World.
Masallacin Eyup Sultan
Masallacin Eyup Sultan, a daya bangaren, ya yi shuhura a matsayin waje mai tsarki ga mutanen da ke son gudanar da ibada a birnin, shi ne aka bayyana a matsayin mafi nutsuwa da zaman lafiya a Istanbul.
"Masallacin Eyup Sultan na daya daga cikin gine-ginen Musulunci mafi tsufa a Istanbul, yana da matukar muhimmanci saboda a nan aka binne wasu Sahabban Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam, da suka hada da Ayyub Al Ansari.
Bayan kwace birnin Istanbul, ayyukan haka da aka yi sun gano wannan kabari, inda aka ba shi girma na musamman.
Haka zalika, yadda wata rana Manzon Allah SAW ya zama bako a gidan Ayyub Al Ansari na kara wa Masallacin wata daraja ta musamman," in ji Ahunbay.
"A tarihi baki daya, Sarakunan Usmaniyya sun yi aiki sosai a wannan waje. Masallacin da ke wajen badalar Istanbul, ya koma wata makabarta mai nutsuwa, har ta kai ga wajen ya zama kamar a ce wurin da mutuwa ke giftawa ne," in ji Ahunbay.
Farfesan ta kara da cewa "Kaburburan muhimman mutane tun daga karni na 16, irin su Sokullu Mehmet Pasa da Siyavus Pasa, tare da cibiyoyin tallafi da taimako da suka kafa, na kara tabbatar da irin lada da jin dadin da mutum zai samu bayan rayuwarsa sakamakon ayyukan alheri da taimako."
Titin Istiklal
Bincike ya tabbatar da titin Istiklal sananne ne da ya zama mafi tattara mutane da yawa saboda kasuwaci, hada-hada da kai komin jama'a a cikinsa.
Makabartar Karacaahmet
A daya bangaren kuma, makabartar Karacaahmet ta zama wajen bakanta rai mafi dadewa da kowa ya sani, ta kai shekara 700 kuma ita ce mafi girma a Istanbul.
Tsaunin Camlica
Tsaunin Camlica na da matsayin kasancewa waje mafi sarari a Istanbul, kamar yadda bincike ya tabbatar.
A watan mayun 2019, an kammala gina masallaci mafi girma a Istanbul da ke iya daukar mutum 57,000 a lokaci guda a wannan tsauni.
Masallacin Sultan Ahmet
Masallacin Sultan Ahmet da aka fi sani da Blue Mosque na nan a daura da Masallacin Hagia Sophia Mai Girma a dandalin Sultan Ahmet. Ana yi wa masallacin kallon waje mafi biyayya a Istanbul, waje da kowa zai iya ji kamar a gida yake.
Ahunbay ta bayyana cewa "Masallacin nan a tsakiyar birnin Istanbul, yana bayyana fasahar gini ta Daular Usmaniyya tare da hasumayoyinsa guda shida.
Haraba mai girman gaske da ke cikinsa na jan hankali da sanyaya zukata. Masallacin ya zama na wakiltar cigaban gini na Daular Usmaniyya, da kuma tuna mana da kwararren magini Mimar Sinan."
Ahunbay ta kara da cewa 'Shiga cikin masallacin kawatacce na sanyaya zukata da bayar da nutsuwa."
Farfesa Ahunbay ta jaddada muhimmancin adana wuraren tarihi, wanda wajibi ne kuma abu da ke bayyana mana yadda jiya ta kasance.
Kiyayewa da kare wadannan kayayyaki na tabbatar da nuna darajar wasu zamanoni da al'adu don amfanin al'ummu na yanzu da na gobe. Abun ya wuce wai kawai na adana kayayyakin, darajarsu ma na da matukar muhimmanci.