Daga Ibrahim Karatas
Tsakanin shekarar 2018 zuwa ta 2022, kason Turkiyya a kasuwar sayar da makamai na duniya ya karu daga kashi 0.6 cikin 100 zuwa kashi 1.1 cikin 100, lamarin da ya mayar da kasar ta 12 a cikin kasashen dake fitar da makamai a duniya.
Masana’antar tsaron Turkiyya tana fadada da sauri irin wanda ba ta taba yi ba cikin shekaru 20 da suka wuce, kuma rahotanni biyu da aka fitar kwanan nan sun nuna matakin da masana’antar makamai na kasar ya kai.
Kamfanonin Turkiyya uku na cikin kamfanonin tsaro 100 da ke kan gaba a jerin a shekarar 2022 a jerin da kafar watsa labarai ta duniya Defense News take fitarwa a kowace shekara.
Yayin da kamfanin Aselsan ya kasance na 49 a jerin sunayen, Kamfanin Turkish Aerospace Industries (TAI) ya zo na 67 yayin da kamfanin Roketsan ya kasance na 86.
A shekarar 2020, jerin sunayen kamfanonin tsaron da ke kan gaba na dauke da sunayen kamfanonin Turkiyya bakwai.
Duk da cewar a halin yanzu kamfanonin da ke cikin jerin sunayen kamfanonin 100 da ke kan gaba ba su kai hakan ba, kason Turkiyya ya karu sosai cikin shekara uku.
Yayin da kudin da kasar ke samu ta sayar da makamai a kasashen ketare ya kai dala bliliyan 2.28 a shekarar 2020, kudin ya karu zuwa dala biliyan 4.3 a shekarar 2022.
A daya bangaren kuma, wani rahoto kan musayar makamai na kasa da kasa a shekarar 2022, wanda cibiyar SIPRI da ke Sweden ta hada, ya nuna cewa makaman da Turkiyya take sayarwa a ketare ya karu da kashi 69 cikin 100 a cikin shekara hudu idan aka kwatanta shekarun 2018 zuwa 2022 da 2013 zuwa 2017.
Kason Turkiyya na kasuwancin makamai na duniya ya tashi daga kaso 0.6 cikin 100 zuwa kaso 1.1 cikin 100 tsakanin shekarar 2018 zuwa 2022, lamarin da ya mayar da kasar ta 12 a cikin kasashen da ake sayar da makamai a duniya.
Bugu da kari, makaman da kasar take shigowa da su sun ragu da kashi 49 cikin 100 idan aka kwantanta lokutan guda biyu.
Yayin da sashen yake kara girma a wani lokaci na rashin tabbas a duniya, kamfanonin makamai na Turkiya za su samu kwan-gaba kwan-baya ta fagen cikini. Duk da girman da masana’antar ke yi sannu a hankali ba shi da makawa.
Yayin da kamfanonin Turkiyya suka samar da kashi 20 kawai cikin 100 na bukatar sojin kasar a shekarar 2004, adadin ya karu zuwa kashi 80 cikin 100 a shekarar 2022.
An samu wannan sauyin mai kyau ne saboda shawara da gwamnatin Turkiyya ta yanke na mayar da masana’antar makamin kasar ta ‘yan kasar kadai a farkon shekarun 2000.
Tun wancan lokacin, kamfanonin Turkiyya sun kera bindigogi da motoci masu sulke da tsarin makami mai linzami ko kuma MANPADs da manyan bindigogi, ire-iren makamai masu linzami da za su iya tafiyar kilomita 1000.
Haka kuma sun kera jirage masu saukar ungula da kananan jiragen yaki da kuma uwa uba ingantattun jirage marasa matuka masu dauke da makamai wadanda sun yi suna a fadin duniya.
A wani bangaren kuma, Turkiyya na dab da fara kera jiragen yakinta da tankokin yaki da kuma manyan bindigogin howitzer, wadanda za su iya samar da karin kudaden shiga.
Kamar yadda sakon kamfanonin da ke kere-kere ya fada, dukkan makaman da ke da wahalar yi za su samu a shekarar 2028.
A farkon watan nan, kamfanin TAI ya fitar da jirgi mara matukinsa na yaki da ya fi inganci, Anka-3, da karamin jirgin yaki da na horaswa mai suna Hurjet, da kuma wani samfuri na biyar na jirgin yakin TFX.
Baya ga kera jiragen sama, wani kamfanin da ke karkashin TAI, TEI, kamfanin kera inji, zai kwada injinsa mai karfin 6000 a ma'aunin lbs.
A cikin wannan shekarar kuma zai fara aiki a kan inji mai karfin 35.000 a ma'aunin lbs ga jirgin yakin TFX, wanda ake tsammanin za a gama a shekarar 2028.
A wani bangaren kuma, kamfani mai kera mota mai sulke BMC zai ba da tankokin yakin Altay guda biyu ga sojin Turkiyya a cikin watan Afrilu kuma zai fara yin motocin da yawa a shekarar 2025.
BMC ya warware matsalar injin ta hanyar sayensa datga Koriya ta Kudu har zuwa lokacin da zai iya amfani da injinsa mai karafa 1500 HP Batu, a shekarar 2026.
Kamfanonin Turkiyya masu kera makami mai linzami da jirgin ruwa, da jirgi mara matuki da motoci da suna tallata hajarsu wadanda ba sa bukatar kayayyaki daga ketare.
Rahotanni sun ce Aselsan, kamfanin tsaro da ya fi girma a Turkiyya, yana da kayayyakin da aka biya shi kudinsu na dala biliyan 7.6 .
BMC zai yi shekara biyu yana samar da motocinsa masu suna kirfi wadanda nakiya ba ta bata su.
Baykar Tech ma ya gaya wa abokan cinikinsa su jira wasu shekaru kafin su samu jirage marasa matukansu.
Bugu da kari, BMC ya ce kasashe da yawa suna son sayen tankin yakin Altay na Turkiyya.
Kuma suna sauraron karin ciniki a lokacin da jiragen yakin TFX suka fara shawagi a sama.
A matsayin misali na karshe, Roketsan ta samu ta kera makami mai linzami da ke iya cimma abu mai nisan kilomita 150 da aka nufa.
Alkaluma sun nuna cewa Turkiyya ta ci gaba a fagen masana’antar tsaro da kananan makamanta mara tsada, wadanda ake kera yawancin abubuwa da ake hada su da su cikin kasar.
Alal misali, masu kera jirgi mara matuki na Turkiyya da makami mai linzami na iya cin gashin kansu yanzu ta yadda takunkumin kasashen waje ba zai iya dakile su ba.
Saboda haka, suna da ‘yancin kerawa tare da tallata makamansu a kasuwar kasa da kasa.
Saboda makaman na ‘yan kasa ne da ingancin makaman Turkiyya za ta iya zama muhimmiyar kasar da ke sayar da makamai mai samun kudin shiga sama da biliyan hudu.
Alal misali, yayin da farashin mota mai sulke yake dala 500.000, ita kuwa tankar yaki ta Altay ta kai dala miliyan 15.
Haka kuma, yayin da ake sayar da jirgi mara matuki na Bayraktar TB2 kan kudi dala miliyan 5, ana sayar da sabon jirgi mara matuki a kan akalla kudi dala miliyan 30.
A karshe, ana tsammanin cewa jirgin yakin TFX jet zai kai kudi dala miliyan 100.
Wannan na nufin cewa sayar da jiragen yaki samfurin TFX zai iya kawo kudi daidai da abin da masana’antar tsaro ta Turkiyya ke samarwa.
Za a iya fahimtar cewa Turkiyya ka iya zama cikin kasashe goma da ke kan gaba wajen sayar da makamai a duniya ta kuma fara samun kudi da ya kai dala biliyan 20 cikin shekara goma.
Saboda haka, baya ga kasancewa mai dogaro da kai wajen samun makamai, zai samo sabbin ayyukan da kudi.
Tasirinsa kuma a kan manufar kasar wajen Turkiyya ba sai an fada ba.
Masana’antar tsaron Turkiyya ta riga ta shiga rige-rigen duniyar. Saboda haka, lallai kamfanonin za su tabbatar da kasar a cikin kasashen da ke kan gaba wajen kera tare da sayar da makamai.