Hoton, wanda aka dauka a zamanin da, ya kafa tarihi, ya nuna yadda wata dattijuwa cike da murmushi a fuskarta ke kokarin kada kuri’arta a cikin akwatin zabe na katako mai girma, yayin da sauran mutane ciki har da masu sanya ido kan zaben suka zura mata ido.
An dauki hotun ne a ranar 21 ga watan Oktoban 1930 yayin da aka gudanar da zaben kananan hukumomi a karon farko a birnin Santambul, a lokacin aka bai wa mata damar shiga cikin harkokin zabe kai-tsaye.
Wani dan jarida mai daukar hoto da ba a bayyana sunansa ba ne ya dauki hoton.
Hoton, mai launin baki da fari, ya kasance hoto na farko da ke nuna tarihin yadda aka kafa sabuwar jamhuriya ta mulki dimokuradiyya a Turkiyya.
Kazalika ya kasance abin gani da kwatance ga yanayin da tsarin dimokuradiyya ke tafiya da zamani a kasar bayan kusan karni biyar da mulkin Daular Usmaniyya.
Za a dauki tsawon wasu shekaru hudu kafin mata a Turkiyya su iya cin zaben gama-gari. Amma duk da haka, ana iya cewa sun yi zarra a zamanin baya idan aka kwatanta da takwarorinsu na yawancin kasashen Turai.
A wani hoto mai launin baki da fari, an ga masu jefa kuri'a sun yi layi a dandalin tarihi na Istiklal da ke Santanbul, a lokacin babban zaben da aka yi a ranar 27 ga Oktoba na 1957.
Wani fitaccen dan jaridar kamfanin dillancin labarai na AP Mario Torrisi ne ya dauki hoton, Moris ya taba daukar hoton mutane irin su Paparoma Paul na shida da kungiyar mawaka da aka fi sani da ‘The Beatles’
A cikin hoton, Torrisi ya hasko wani bangare na yadda rayuwa ta kasance a shekarun 1950 a Santanbul, inda 'yan garin sanye da kwat da riguna suke wucewa ta gaban wasu shaguna da ke gundumar Istiklal. Wasu daga cikin kyawawan tsararrun gine-ginen da aka gani a cikin hoton har yau suna nan a tsaye.
An ga wani gunkin karamin jingin kasa kusa da wata mota samfurin Volkswagen da aka fara kerawa a shekarar 1950, wanda yana cikin abubuwan da aka hasko a cikin hoton.
A shekarun 1950 Turkiyya ta kasance karkashin jagorancin Adnan Menderes wanda jam'iyyar adawa ta ‘yan Democrat ta ci galaba a kan jam'iyyar Republican People's Party CHP, shekaru bakwai kafin zaben 'yan majalisar dokoki na ranar 14 ga Mayu na 1950.
A zaben 1957, Menderes ya zargi jam'iyyarsa da yanke hukunci har sau uku kan jam'iyyar CHP da ke karkashin jagorancin Ismet Inonu.
Sai dai shekaru uku bayan haka, jamhuriyar ta fuskanci juyin mulkin farko da ya tilastawa kifar da mulkin Menderes. Daga baya gwamnatin mulkin soji ta rataye shi.
Sakamokon irin yadda tarihin Turkiyya ya kasance da yadda aka yi ta samun kwan-gaba- kwan-baya tsakanin jam'iyyun siyasa, 'yan kasa sun ci gaba da kasancewa a gaba da kuma tsakiyar siyasar kasar.
Yawancin wadannan lokutai masu mahimmanci sun zama tarihi da za a iya tunawa da su a yanzu, godiya ta musamman ga ‘yan jaridan da suka ba da shaida wajen ajiye tarihin abubuwan da suka faru a zamnain baya.
A ranar 28 ga watan Mayun 2023 ne masu kada kuri'a a Turkiyya za su sake fitowa rumfunan zabe domin kada kuri'unsu na zaben shugaban kasar da za a yi tsakanin shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan da babban abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu.
Ga yadda aka gudanar da zaben Turkiyya na tsawon shekaru cikin wasu hotuna.
Zabe a birnin Santanbul na 1935
Babban zaben kasa na 1938
Ranar Matasa da wassani na 1943
Babban zaben kasa na 1950
Babban zaben 1957
Babban zaben 1961
Yakin Zabe na cikin gida a 1985
Zaben 1994 na Santanbul
Babban zaben 1999
Babban Zaben 2002
Babban Zaben 2007
Zaben Shugaban Kasa na 2014
Babban Zaben watan Yunin 2015
Kuri'ar Raba Gardama Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki a 2017
Zaben Shugaban Kasa da 'Yan Majalisar Dokoki na 2018