Sojojin ruwan Turkiyya sun gano akalla abubuwan fashewa 28 da ake zargi a cikin tekun Bahar Aswad, a cewar hukumomin kasar.
Binciken da rundunar tsaron karkashin ruwa ta gudanar ya nuna cewa abubuwan da aka gano bama-bamai ne da ba su fashe ba, kamar yadda ofishin gwamnan Istanbul ya bayyana a wata sanarwa da aka fitar.
A ranar Lahadi ne wata tawaga ta masu ninkaya ta kwaso wasu daga cikin abubuwan da aka killace a wani wuri da ke da tsaro a yankin arewa maso gabashin lardin Istanbul bayan rahotannin da aka samu na kasancewarsu a wajen kwanaki biyu kafin lokacin.
“An gano akalla alburusai guda 28, tare da ciro takwas daga cikinsu, wadanda aka iya fitowa da su daga cikin ruwan, an kuma mika su ga rundunar ‘yan sandan SAS domin tantancewa da lalata su,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa har yanzu dakarun tsaron karkashin ruwa na ci gaba da aikin mamaye yankin.
Kazalika sanarwar ta ce za a gudanar da aikin fasa bama-baman ranar Laraba "bayan an bi duk wasu matakai na tsaro da suka kamata."