Domin tunawa da daya daga cikin wadanda suka taka rawa a bangaren ilimin taurari na Turkiyya, Google ya karrama Nuzhet Gokdogan ta hanyar saka ta a tambarinsa inda yake yabata a matsayin daya daga cikin mata masana ilimin taurari na farko a kasar.
An haife ta a ranar 14 ga watan Agustan 1910 a Santambul, Gokdogan ta nuna basirarta ta bangaren harsuna, inda ta kware a Faransanci da Jamusanci da Turkanci.
Ta yi karatu a Jami’ar Lyon da ke Faransa, inda ta yi karatun digirinta na farko a lissafi.
Karatunta na boko ya kai wani mataki a 1933 inda ta samu shaidar digiri a bangaren falsafa daga Jami’ar Paris.
A Paris din, ta ci gaba da bincike da kuma yanke shawarar komawa kasarta ta gado wato Turkiyya.
Sakamakon matukar sha’awar ilimin taurari, Gokdogan sai ta mayar da kwarewarta ta fannin ilimi.
Sai da ta kai matakin Farfesa a Cibiyar Ilimin Taurari da ke Sashen Nazarin Ilimin Taurari a Tsangayar Kimiyya ta Jami’ar Santambul.
Shigarta cibiyar wani muhimmin lokaci ne sakamakon kayayyakin koyarwa da kuma koyarwar da ake yi da harsunan waje kamar su Ingilishi da Jamusanci.
Gokdogan, sakamakon gogewarta a harsuna, sai ta yi gaba domin cike gibi, inda ta fassara litattafai shida wadanda suka shafi yanayin taurari.
A cikin shekarar 1937, ƙwarewar ilimi ta Gokdogan ta haskaka a cikin karatunta game da abubuwan duhu da ke kewaye da rana, wanda a karshe har ta samu digirin digirgir.
Hankalinta ya kara tashi a lokacin da ta hau babban matsayi na farfesa a jami'ar Istanbul. Likkafarta ta kara gaba a lokacin da ta samu matsayin Farfesa a Jami’ar Santambul.
Mace shugabar tsangayar jami’a ta farko a Turkiyya
An samu sauyi a 1954 a lokacin da Gokdogan ta zama shugabar tsangayar kimiyya, inda ta zama ta farko da ta taba rike irin wannan mukamin a tarihin kasar.
Gudunmowar da ta bayar ta wuce ta cikin aji, saboda ta rubuta takardun kimiyya da dama ga jaridun kasar, inda ta kuma rubuta litattafai uku na bangaren ilimin taurari da lissafi da sararin samaniya.
Kasancewarta ta zama ja gaba a wannan bangare ya sa ta kawo ci gaba a fannin ilimin taurari a kasar, inda har ta kirkiro kungiyoyi da dama kuma masu tasiri.
Daya daga cikinsu, Gokdogan ta bayar da gudunmowa wurin kafa Kungiyar Ilimin Taurari ta Turkiyya, da Kungiyar Mata a Jami’o’i da Kungiyar Ilimin Lissafi ta Turkiyya, wadanda kungiyoyi ne da ke ci gaba da bayar da gudunmowa a Turkiyya.