Wani yunƙuri na nuna goyon baya ga al'ummar Gaza na ci gaba da samun karɓuwa a Turkiyya, a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a yankin Gaza na Falasdinu tsawon wata guda, tare da kashe aƙalla Falasdinawa 10,500.
Daidaikun mutane da kamfanoni da kungiyoyin al'umma da masu zaman kansu sun kasance suna juyawa kayayyakin Isra'ila baya suna maye gurbinsu da wasu, don nuna adawa da yaƙin da Isra'ilan ke yi da Gaza.
"Bayan kisan kiyashin da Isra'ila take yi wa Falasdinawa a Gaza, ya zama wani al'amari muhimmi a yanke hulɗa da hanyoyin da ke samar da kudade ga kasar," in ji wata mai zane a Istanbul Feride Karatas, wadda ta shiga sahun ƙaurace wa Isra'ila a hirarsa da TRT World.
"Ina da 'ya'ya biyu; Ba zan iya kallon yara a Falasdinu suna shan wahala, suna cikin tsoro da rawar jiki da kuka ba tare da taimako ba, su kaɗai. ... Shi ya sa ni da ƙawayen da ke kusa da ni muke ƙoƙarin yin duk abin da za mu iya,” in ji ta
Ba tare da wata tangarda ba, miliyoyin al'ummar Turkiyya ma sun fara ƙauracewa tsarin amfani da katunan Visa da Mastercard - domin rage kamashon da kamfanonin ke samu daga hada-hadar katunan.
A gefe guda kuma, mutane a faɗin Turkiyya sun ƙara nuna sha'awarsu ga amfani da TROY wanda Turkiyya ta samar, wanda ke nufin "Türkiye's Payment Method” wato "Hanyar Biyan Kuɗi ta Turkiyya" Karatas na ɗaya daga cikin waɗannan mutanen.
Da samun labarin TROY, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen sauyawa zuwa amfani da shi, tare da kwaɗaitar da jama'arta yin hakan.
"Haƙiƙa ƙauracewa kayayyakin mutum ɗaya yana da muhimmanci. Amma babban tushen samun kudin kasar nan shi ne katin Mastercard da Visa da muke amfani da su kusan kowace rana," in ji ta.
Karatas ta ƙara da cewa, wani kamasho na tafiya ne ga kamfanonin da ke tallafa wa Isra'ila daga kowane amfani da aka yi da katin Mastercard da Visa, ko da kuwa 'yan kasar za su ci dinga amfani da su ne kawai ta wajen sayen kayayyakin cikin gida, Karatas ta ƙara da cewa: "Babbar ƙauracewa ita ce yanke wannan hanyar samun kudin shiga."
Sama da Falasdinawa 10,500 aka kashe
A cikin makon da ya gabata, TROY ya kasance wani muhimmin abu na fafutuka a shafukan sada zumunta.
A ranar Talata, kamfanin TROY ya ba da sanarwar cewa adadin katunanta da ake hada-hada da su sun kai miliyan 19, kuma an samu hauhawar yawan sayayya da shi a cikin watan da ya gabata.
Ummehan Peker, ƙwararriya kan halayyar ɗa'adam, na cikin waɗanda suka sami labarin TROY ta a kafafen sada zumunta.
Ta shaida wa TRT World cewa ta koma tsarin Turkiyya ne domin ta ƙaurace wa Isra'ila, kuma saboda tana son tallafa wa kamfanin cikin gida.
"Wannan shawara ce mai sauƙi, zaluncin da ake yi wa Falasdinu ya daɗe yana damuna... Bisa la'akari da halin da ake ciki a yau, ganin cewa Mastercard da Visa suna goyon bayan Isra'ila sosai ya isa dalili, kuma kasancewar TROY na cikin gida ne ya sake ƙarfafa ni zaɓarsa," ta ce.
Muguntar da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, da rashin son amsa kiran zaman lafiya da tsagaita wuta, ya haifar da gagarumin ƙaurace mata a Turkiyya.
Tun daga jami'o'i har zuwa ƙananan hukumomi, kungiyoyi na gwamnati da masu zaman kansu sun dakatar da sayar da kayayyaki daga kamfanonin da ke goyon bayan Isra'ila, sakamakon ayyukan cin zalin da kasar ke yi a Gaza.
Lardin Corum, a karon farko ta yi wani ƙoƙari na musanya katunan kuɗi na ma'aikatanta sama da mutum 2,000 daga Visa da Mastercard zuwa TROY.
Magajin garin lardin, Halil İbrahim Aşgın ya jaddada cewa kashi 1.5 cikin 100 na duk wani ciniki ta hanyar Visa da Mastercard na tafiya ne zuwa Isra'ila da kuma wadanda suka amince da mamaye yankunan Falasdinawa.
Shahararren kamfanin jiragen sama na Turkiyya shi ma ya bi sahun ƙaurace wa kayayyakin da Isra'ila ke yi daga cibiyoyinsu da suke cikin gida.
Majalisar Dokokin Turkiyya ta kuma sanar a ranar Talata cewa, ba za ta ƙara amfani da kayayyakin kamfanonin da ke goyon bayan ta'addancin Isra'ila ba.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 10,500 a wasu hare-hare ba ƙaƙƙautawa da take kaiwa Gaza - yankin da ke da mazauna miliyan 2.3.
Kimanin kashi 40 cikin 100 na wadanda aka kashen yara ne, a cewar jami'ai.