Turkiyya ta zama babbar hanyar da masu neman mafaka ke bi don tsallaka wa zuwa Turai da nufin fara sabuwar rayuwa, musamman wadanda ke guje wa yaki da cutarwa. /Hoto: AA

Turkiyya ta kuɓutar da baƙin-haure 37, ta kuma kama wasu 143 a farmakai daban-daban, in ji Dakarun Tsaron Gabar Tekun kasar.

An kuɓutar da baƙin-haure 20 da suka haɗa da yara bayan da jami'an tsaron tekun Girka suka kore su daga iyakar tekun ƙasar a yankin Bodrum da Mugla, in ji Rundunar Tsaron Tekun Turkiyya a ranar Laraba.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kuɓutar da ƙarin wasu 'yan gudun hijira su 17 da su ma Girka ta kora daga iyakarta ta teku.

Ankara da ƙungiyoyin kare hakkokin ɗan'adam sun sha sukar Girka bisa wannan abu da ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa na korar baƙin-haure a teku maimakon kuɓutar da su. Hakan na jefa rayuwar mutanen da suka haɗa da yara ƙanana cikin hatsari.

A Mugla, an tare rukuni biyu na baƙin-hauren. Dakarun Tsaron Tekun sun dakatar da wani jirgin ruwan balan-balan a Bodrum, tare da kama baƙin-haure 33 da suka haɗa da yara 16. Kazalika an sake kama wasu su 35 da suka haɗa da yara kanana 13 a Mugla.

A gundumar Eceabat da ke lardin Canakkale, an kama 'yan gudun hijira 21 da suka hada da yara biyar. A kusa da gundumar Kusadasi da ke lardin Aydin kuma, an tare wasy 'yan gudun hijirar 18 da suka hada da yaro daya da wani da ake zargin mai fataucin mutane ne. A Urla kuma an tsayar da wani jirgin ruwan roba ɗauke da baƙin-haure 36 da suka haaɗ da yara ƙanana 13.

Turkiyya ta zama babbar hanyar da masu neman mafaka ke bi don zuwa Turai da nufin fara sabuwar rayuwa, musamman waɗanda ke guje wa yaƙi da cutarwa.