Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar ''kawarwa' wajen nuna 'yan ta'addan da suka mika wuya ko kuma aka kashe su ko kuma aka kama su.  / Hoto: AA      

Hukumar leƙen asiri ta Turkiyya MIT ta ''kawar'' da wata babbar ƴar ta'addar PKK/KCK a yankin arewacin Iraƙi, wacce ke da alhakin ɗaukar yara ƙanana zuwa cikin ƙungiyar ta'addancin, a cewar majiyoyin tsaro.

Hukumar MIT ta kai samamen yaƙi da ayyukan ta'addaci kan iyakokin ƙasar da nufin kamo Gulsun Silgir wacce aka fi saninta da Sara Hogir Riha.

Ƴar ta'addan ita ke da alhakin aiwatar da ayyukan ta'addanci tun daga shekarar 2011, ciki har da yaudarar matasa zuwa ƙungiyar ta'addanci ta PKK, a cewar majiyoyin, waɗanda suka buƙaci a sakaya sunansu saboda ba a ba su damar magana da kafafen watsa labarai ba.

Kazalika an tabbatar da cewa Silgir ta yi aiki a yankin Sulaymaniyah na Iraƙi tun daga shekarar 2021.

Majiyar ta ƙara da cewa, an kai mata hari ne a gundumar Penjwin da ke yankin Sulaymaniyah na ƙasar Iraƙi.

Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar ''kawarwa'' wajen bayyana 'yan ta'addan da ake magana a kai wadanda suka miƙa wuya ko aka kashe su ko kuma aka kama su.

Ƴan ta'addan ƙungiyar PKK suna yawan fakewa a arewacin Iraƙi domin shirya kai hare-haren wuce gona da iri a Turkiyya.

A watan Afrilun 2022 ne Turkiyya ta ƙaddamar da Operation Claw-Lock domin kai hari kan maɓoyar 'yan ta'addan PKK a yankunan arewacin Iraƙi waɗanda suka haɗa da Metina da Zap da kuma Avasin-Basyan kusa da kan iyakar Turkiyya.

A sama da shekaru 35 da ta kwashe tana aiwatar da ayyukan ta'addanci a kan Turkiyya, ƙungiyar PKK - wadda Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai EU suka sanya ta a jerin ƙungiyoyoin ƴan ta'adda - ita ce ke da alhakin mutuwar mutum fiye da 40,000 da suka haɗa da mata da yara da har ma da jarirai.

TRT World