Shugabannin duniya da gwamnatoci suna ci gaba da aika saƙon ta'aziyya da jaje ga Turkiyya sakamakon gobarar da ta kama a wani wajen wasa a dusar kankara da a kalla mutane 76 suka mutu, wasu 51 kuma suka samu raunuka.
Turkiyya ta sanar da zaman makoki na rana guda a ranar Laraba sakamakon rasa rayuka a gobarar da ta kama otel din na lardin Bolu da ke arewa maso-yammacin ƙasar a ranar Talata.
Ƙungiyar Ƙawancen Ƙasashen Turkawa ta yi ƙasa-ƙasa da tutocin ƙasashen tare da bayyana goyon baya ga jama'ar Turkiyya.
"Mun yi baƙin ciki matuƙa da wannan mummunan labari, kuma muna miƙa saƙon ta'aziyya da jaje ga iyalan waɗanda suka mutu. Muna fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata," in ji ƙungiyar.
Shugaban Ƙasar Kazakhistan, Kassym-Jomart Tokayev ya aika da saƙon ta'aziyya ga Turkiyya sakamakon ibtila'in da fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
Shugaban Ƙasar Ukraine Vladimir Zelensky ma ya ce suna matuƙar baƙin ciki da afkuwar gobarar, kuma ya miƙa ta'aziyya ga shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
"Ina fatan samun sauƙi ga duk waɗanda suka jikkata. Ukraine na jin irin raɗaɗin da jama'ar Turkiyya ke ji a wannan mawuyacin hali," in ji Zelensky a wani saƙo ta shafin X.
Firaministan Jamus Olaf Scholz ya bayyana "tsagwaron baƙin ciki" bisa mutuwar mutane da dama sakamakon gobarar. "Tunanina na tare da iyalan waɗanda suka mutu kuma ina fatan samun sauƙi ga waɗanda suka samu raunuka," ya rubuta a shafinsa na X.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Syria ma ta mika sakon ta'aziyya a wata sanarwa da ta fitar ta shafin X, "Jama'ar Turkiyya sun kasance tare da mu a koyaushe muka shiga tsanani, kuma yau, Syriyawa na tare da 'yan'uwansu na Turkiyya, muna fatan samun waraka daga wannan mawuyacin hali."
China ma ta aike da saƙon ta'aziyya da jaje ga "waɗanda ibtila'in ya rutsa da su" da ma iyalansu, kuma ta yi fatan samun waraka ga waɗanda suka jikkata.
Iran ma ta aike da sakon ta'aziyya da jaje ga Turkiyya. Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ya yi addu'ar samun "jinƙai da gafarar Ubangiji" ga waɗanda lamarin ya rutsa da su.
"Tunaninmu na tattare da iyalan waɗanda suka mutu da duk waɗanda ibtila'in ya rutsa da su. Muna fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata," in ji shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagame.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ma ta fitar da sanarwa ta shafin Facebook, tana bayyana saƙon ta'aziyya da jaje ga Turkiyya, ma'aikatar ta yi fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata.