Masu kaɗa ƙuri'a a Turkiyya suna ta shirin gudanar da zaɓuka masu muhimmanci da za a yi ranar 31 ga watan Maris.
Hukumar Ƙoli ta Zaɓe (YSK) ta sanar da sunayen jam'iyyu 36 da suka cancanci fafatawa a zaɓukan.
Wasu daga cikin jam’iyyun da ke fafatawar sun haɗa da Justice and Development (AK) da Jam’iyyar Nationalist Movement Party (MHP) da Jam’iyyar Republican People’s Party (CHP) da IYI Party da Grand Union Party (BBP) da New Welfare Party (Yeniden Refah) da jam'iyyar DEM, da kuma Saadet da jam'iyyar Demokrat.
Sakamakon zabukan da aka gudanar na ƙananan hukumomi a manyan biranen kasar Turkiyya guda uku - Istanbul da Ankara da Izmir - shi ne sakamakon da ake sa ran za a yi a wadannan zabukan.
A Istanbul, Murat Kurum, wanda shi ne dan takara na farko a jam'iyyar AK mai mulki, zai fafata da Ekrem Imamoglu, Magajin Gari mai ci daga babbar jam'iyyar adawa ta CHP.
A birnin Ankara manyan ƴan takarar sun haɗa da Turgut Altinok na jam'iyyar AK da kuma Mansur Yavas na jam'iyyar CHP. Hakazalika wadanda ke kan gaba a gasar a Izmir su ne Hamza Dag daga jam'iyyar AK Party da kuma Cemil Tugay na jam'iyyar CHP.
Sama da sabbin masu jefa kuri'a miliyan guda
Daga cikin mutum 61,441,882 da suka cancanci kaɗa ƙuri’a a wadannan zabuka, 1,032,610 matasa ne da za su iya kada kuri’a a karon farko, a sama da rumfunan zabe 206,000 da za a kafa a fadin kasar.
Zaben da ke tafe zai bayyana kantomomi na larduna 81, gundumomi 973 da na garuruwa 390, tare da mukhtars 50,336. Za su kuma zabar membobin babban majalisun larduna da na gundumomi.
Duk dan kasar Turkiyya da ya kai shekaru 18 a ranar zabe, yana da damar kaɗa kuri'a.
A ranar 29 ga watan Maris ne aka shirya kammala rabon bayanan masu kaɗa ƙuri’a, wanda aka fara a ranar 29 ga watan Fabrairu. Sannan ba za a buƙaci masu kada kuri’a su je rumfar zaɓe da takardunsu ba.
Masu jefa ƙuri'a za su iya duba shafin intanet na hukumar zaɓe ta YSK, da kuma shafin e-Government, da manhajar YSK da kuma kiran YSK a lambar "444 9 975", don gano wurin da akwatin zaɓensu yake inda aka yi musu rajista don jefa ƙuri'a. .
Awannin kaɗa ƙuri'a
Sakamakon sauyin yanayi na lokutan faɗuwar rana a cikin watan Maris, YSK ta ƙara awa guda a kan lokacin zaɓen a larduna 32 na gabashin ƙasar.
Amma a larduna irin su Adiyaman, Agri, Artvin, Bingol, Bitlis, Diyarbakir, Elazig, Erzincan, Erzurum, Gaziantep, Giresun, Gumushane, Hakkari, Kars, Malatya, Kahramanmaras, Mardin, Mus, Ordu, Rize, Siirt, Sivas, Trabzon, Tunceli , Sanliurfa, Van, Bayburt, Batman, Sirnak, Ardahan, Igdir, da Kilis, kuma a gidajen gyaran hali a wadannan larduna, sa'o'in kada kuri'a za su kasance daga 07:00 zuwa 16:00.
A wasu larduna, za a gudanar da zabe daga karfe 08:00 zuwa 17:00 agogon kasar.
A lardunan gabas, inda sa'o'in kada kuri'a ke farawa daga karfe 07:00 zuwa 16:00, ba za a iya fara kidayar kuri'u kafin karfe 4 na yamma ba. A wasu larduna, ba za a iya farawa kafin ƙrfe biyar ba. Ko da duk masu kada kuri’a sun kammala yin zabe, ba za a bude akwatunan ƙuri'un ba kafin sa’o’in zaben su ƙare.
A cikin ƙananan hukumomi, za a ƙidaya kuri'un magajin gari da mambobin majalisa, da kansiloli kuma za a ƙidaya su bi da bi.
Sabanin haka, a wasu larduna, za a kirga kuri'un magajin gari da mambobin majalisar gundumomi da mambobin majalisar lardi da kansiloli da kuma kirga su bi da bi.