1430 GMT —An ƙidaya fiye da kashi 51 na ƙuri'u — Shugaban YSK Yener
Shugaban Majalisar Ƙoli ta Zaɓen Turkiyya (YSK), Ahmet Yener, ya ce, "zaɓen, wanda mutum fiye da miliyan 61 da dubu 441 da 882 suka jefa ƙuri'unsu a akwatunan zaɓe dubu 207 da 848, inda jam'iyyu 34 suka fafata, an kammala shi cikin nasara idan ban da ƴan ƙananan ƙorafe-ƙorafe.
“An soma ƙidaya ƙuri'u kuma sakamakon ya soma shiga babban rumbun ajiye bayanai,” a cewar Ahmet Yener.
"Majalisa za ta gana nan ba da jimawa game da wannan batu don amincewa kan lokacin da za a ɗage haramcin hana wallafa bayanai kan zaɓe."
1400 GMT — An soma ƙirga ƙuri'u bayan kammala zaɓen yankuna a Turkiyya
An kammala jefa ƙuri'a a zaɓukan magadan birane da na sauran wakilai a faɗin ƙasar Turkiyya.
An buɗe rumfunan zaɓe da misalin ƙarfe 8 na safe (0500GMT) sannan aka rufe da ƙarfe 5 na yamma (1400GMT) a galibin yankunan ƙasar.
Bisa dalilai na yanayi da jinkirin faɗuwar a watan Maris, Majalisar Ƙoli ta Zaɓen Turkiyya, YSK ta ƙara lokacin zabe da awa ɗaya a larduna 32 na gabashin ƙasar.
An buɗe rumfunan zaɓen da misalin ƙarfe 7 na safe zuwa huɗu na yamma (1300GMT).
1030 GMT —Zaɓukan yankuna za su buɗe 'sabon babi ': Shugaba Erdogan
Zaɓukan magadan birane da na larduna za su "buɗe wani sabon babi a wannan ƙasa tamu”, a cewar shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan bayan ya kaɗa ƙuri'arsa tare da mai ɗakinsa Emine Erdogan a Istanbul.
Erdogan -- wanda ya soma harkokin siyasarsa da riƙe muƙamin magajin birnin Istanbul 1994 -- ya yi tsokaci kan zaɓen majalisar dokoki da na shugaban ƙasa da aka yi a shekarar da ta wuce sannan ya yi fatan cewa "waɗannan za su buɗe sabon babi da kuma sabon ƙarni a ƙasarmu.”
Bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a yankin Uskudar, Erdogan ya jaddada muhimmancin yin zaɓe, yana mai yin kira ga dukkan waɗanda suka cancanci jefa ƙuri'a su "fito domin zaɓar wanda suke so. "
0500 GMT — An soma kaɗa ƙuri'a a zaɓukan yankuna na Turkiyya
Ƴan ƙasar Turkiyya sun soma jefa ƙuri'unsu ranar Lahadi a zaɓukan magadan birane da na wakilan gundumomi da sauran wakilai da za su kwashe shekaru biyar masu zuwa a kan mulki, ciki har da zaɓukan da ake fafatawa mai zafi a birane irin su Istanbul, Ankara, da Izmir.
An soma zaɓe da misalin ƙarfe 7 na safe kuma za a rufe rumfunan zaɓen da misalin ƙarfe 4 na la'asar a larduna 32 na gabashin ƙasar, yayin da a sauran yankunan ƙasar aka fara kaɗa ƙuri'a da misalin ƙarfe 8 na safe inda za a rufe da ƙarfe 5 na yamma.
A zaɓukan yankunan na ranar 31 ga watan Maris, fiye da mutum miliyan 61 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓe sama da 200,000 da ke faɗin ƙasar inda jam'iyyu 34 suka tsayar da ƴan takara.
Manyan jam'iyyun su ne, jam'iyyar Justice and Development (AK) mai mulki, da babbar Jam'iyyar hamayya ta Republican People's Party (CHP), da Jam'iyyar Nationalist Movement Party (MHP), da Jam'iyyar the Good (IYI) Party, da kuma Jam'iyyar the Peoples' Democratic Party (DEM Party).
Masu zaɓe za su kaɗa ƙuri'unsu ne kawai a yankunansu. Matasa fiye da miliyan 1.32 za su yi zaɓe a karon farko a rayuwarsu.
Ƴan takara 49 ne suke fafatawa domin zama Magajin Birnin Istanbul— Cibiyar Daular Usmaniyya.
Ana amfani da akwatunan jefa ƙuri'a na tafi-da-gidanka guda 1,000 a domin bai wa marasa lafiya damar yin zaɓe.
Ranar zaɓe, an haramta sayar da duk wani nau'i na barasa a bainar jama'a daga ƙarfe 6 na safe zuwa 12 na dare.
Kazalika an haramta wa gidajen rediyo da sauran kafafen watsa labarai yin tsokaci ko hasashe kan sakamakon zaɓen har sai ƙarfe 6 na yamma a agogon ƙasar (ƙarfe uku a agogon GMT).
Daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 9 na dare (ƙarfe uku zuwa shida na yamma a agogon GMT), za a watsa labaran da suka shafi zaɓen ne kawai daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa wato Supreme Election Council (YSK).