Irak'ta Paskalya ayini / Photo: AA

Kiristoci a lardin Hatay na kudancin Turkiyya sun gudanar da bukukuwan Ista, duk da cewar har yanzu suna ci gaba da farfadowa daga radadin girgizar kasar ta afku a yankin.

Sakamakon yadda girgizar kasar ta rushe cocin Katolika da ke gundumar Iskenderun a lardin na Hatay, an gudanar da bikin na bana a Cocin Siant Peter, cocin cikin kogo ta farko a duniya.

Pasto Antuan Ilgit, shugaban Kiristocin yankin ne ya jagoranci bikin na Istar bana, ya kuma bayyana yadda a wannan karon suka sha wahalar shirin bikin saboda girgizar kasar da aka fuskanta.

Hukumar UNESCO ta ayyana Cocin kogo ta Saint Peter da ke tsaunin Staurin a matsayin irin ta ta farko a duniya kuma wadda aka samar a tskaanin 38-39 Miladiyya.

Garin Antakya na lardin Hatay na dauke da marasa rinjaye mabiya addinin Kirista da ke bin dariku daban-daban da suka hada da Syriac mabiya Orthodox da Katolika.

AA