Ana ganin Tuchel a matsayin wani karamin dodon Guardiola / Photo: AFP

A yayin da ake shirin dawowa wasanni cin kofin Zakarun Turai a ranar Talata, wasan da zai dauki hankali shi ne wanda za a yi a Etihad, inda Manchester City za ta karbi bakuncin Bayern Munich daga Jamus.

A wannan zagaye na kusa da na karshe na cin kofin Zakarun Turai, kungiyoyi takwas ne za su kece raini cikin zango biyu, domin fitar da guda hudun da za su nemi fitowa wasan karshe na cin kofin.

Daga kungiyoyin guda takwas da suka rage, akwai uku daga kasar Italiya, wato Napoli da Inter Milan da AC Milan, sai biyu daga Ingila, wato Manchester City da Chelsea.

Sai kuma sauran kasashe masu kulob dai-dai, wato Real Madrid daga Sifaniya, da Bayern Munich daga Jamus, sai kuma SL Benfica daga Portugal.

Wasan da Bayern za ta kara da Manchester City zai zamo wasa na farko da Tuchel zai jagoranci kungiyar ta Jamus a kofin Zakarun Turai.

Ana ganin akwai zazzafar hamayya tsakanin kociyoyin biyu, kasancewar sun kara sau 10 a baya bayan nan, yayin da suke jagorantar mabambantan kungiyoyi a Jamus da Ingila, har da ma wasannin karshe a Turai.

A baya dai shi kansa Guardiola ya rike ragamar kungiyar ta Beyern a lokacin da shi kuma Tuchel yake jagorancin kungiyar Mainz. A wannan karo na farkon haduwarsu, Guardiola ya yi galaba kan Tuchel har a sau biyu.

Haka nan, bayan da Tuchel ya koma kungiyar Borussia Dortmund, Guardiola ya sake galaba kansa a karo na uku. Amma a karawarsu ta hudu, sai suka yi canjaras, ba tare da kowa ya zura kwallo ba.

Sai dai ba a dade ba jaruman biyu suka sake haduwa amma wannan karon a wasan karshe na cin kofin DFB-Pokal na Jamus. A wannan karawar ta biyar tsakaninsu, Guardiola ya sake lashe wasan bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Labarin ya fara sauyawa bayan da Tuchel ya koma jagorancin kungiyar Chelsea ta Ingila, shekaru biyar bayan Guardiola yi yi kaura zuwa Ingilar, inda yake jagorantar kungiyar Manchester City.

Kididdiga ta nuna cikin kusan shekaru 10, Guardiola ya samu nasara kan Tuchel har sau shida, yayin da Tuchel ya yi nasara sau uku, duka lokacin yana jagorantar Chelsea a Ingila.

TRT Afrika