Edgar le ya buga wa Barcelona wasa a 2012. / Hoto: Getty Images

Ana zargin ɗan wasan ƙungiyar Dinamo Bucharest, Edgar le, da tura abokin tagwaitakarsa ya buga masa wasa. Edgar le ya buga wa Barcelona wasa a 2012.

Rahotanni daga jaridun ƙasar Romania sun bayyana cewa Edgar, wanda ya koma buga wasa a Dinamo Bucharest, amma daga baya ya fara turo ɗan'uwansa Edelino zuwa ƙungiyar maimakon buga wasan da kansa.

Edgar Ie, mai shekaru 30 a duniya bai samu buga wasannai da yawa ba a makonnin nan saboda rashin ƙoƙari, duk da cewa shi ke karɓar albashi mafi girma a ƙungiyar. Yana shan suka a ƙasar.

Abin da ya ƙarfafa zargin shi ne salon da ya ɗauka na yin magana tare da sauran 'yan wasa da harshe Portuguese kawai.

Bincike

Tuni hukumomin ƙungiyar sun nemi ɗan wasan ya bayar da ƙwayar halittar DNA ɗinsa bayan zargin cewa ɗan tagwayen Edgar, wato Edelino ya buga wasanni aƙalla biyar.

Idan aka tabbatar da zargin, za a iya hukunta Dinamo Bucharest da zaftare maki, wanda zai iya janyo ƙungiyar ta sauka daga gasa ajin ƙwararru.

Bayan fara buga wa Barcelona wasa a 2012, Edgar Ie ya shiga babbar ƙungiyar ƙarƙashin koci Luis Enrique a Disamban 2014. A baya ya buga wa ƙungiyoyin Lille, da Nantes, da Trabzonspor, da Feyenoord, da Basaksehir ta Turkiyya.

Shi kuwa abokin tagwaitakarsa, Edelino le ya kwashe yawancin wasanninsa a ƙaramar gasar ƙasar Portugal.

TRT Afrika