Bayan Leeds United, wadda ke fuskantar barazanar fita daga gasar Firimiya ta dauko Sam Allardyce, kocin ya ce yana mataki daya da kocin Man City, Pep Guardiola da na Arsenal Mikel Arteta da na Liverpool, Jurgen Klopp a kwarewa.
“Ina da shekara 68 kuma na yi kama da tsoho, amma babu wanda yake gaba da ni a harkar kwallon kafa. Pep da Klopp da kuma Arteta ba su kai ni ba,” in ji Allardyce.
Bayan wannan kalaman ne kocin City, Pep Guardiola ya tabbatar da maganar Sam Allardyce.
Leeds United, da ta dauki Sam aiki zuwa karshen wannan kakar gasar Firimiya, tana mataki na 17 da maki 30 a teburin gasar Firimiya yayin da Nottingham Forest mai bin ta ke mataki na 18 a teburin Firimiya da maki 30.
Everton na mataki na 19 a teburin Firimiya da maki 29. Ita kuwa Southampton tana da maki 22.
Kungiyoyi uku da suka kasance a kasan teburin gasar a karshen kakar gasar ne za su koma gasar kasa da gasar Firimiya.
Wannan ne ya sa wasu ke shakku kan ko Sam Allardyce zai iya ceto Leeds United daga fita daga gasar Firimiya.
Tarihinsa na ceton kungiyoyi a gasar Firimiya
A 2001 ne Sam ya fara kubutar da kungiyoyi daga zamewa daga gasar Firimiya. Kungiyar Bolton Wonderers ta kubuta daga fita daga gasar sakamakon kokarinsa.
A kakar shekarar 2008/2009 ne Sam ya fara suna a matsayin mai kubutar da kungiyoyi daga fita daga gasar Frimiya a lokacin da aka nemi ya taimaka wa Blackburn Rovers.
Blackburn ta tsira a gasar Firimiya a wannan kakar.
A kakar 2015-2016 a lokacin da Sunderland ke fuskantar barazanar ficewa daga gasar Firimiya, Sam suka kira. Kuma bai ba su kunya ba. Ya taimaka wa kungiyar ta cigaba da kasancewa a gasar.
Sai dai a kakar 2020/2021 da West Brom ta nemi taimakon Sam, ya kasa ceto ta daga fita daga gasar Firimiya.
Shin Sam zai iya maimaita kwarewarsa a ceto kugiyoyi a wannan karon?
Ranar Asabar ne za a fara ganin kamun ludayin Sam a Leeds United a lokacin da zai kara da yaran Pep Guardiola, Manchester City.
Manchester City ce take saman teburin Firimiya a halin yanzu da maki 79 duk da cewa tana da kwantan wasa daya.
City tana neman tabbatar da matsayinta a saman gasar Firimiya ta hanyar yin nasara a karawar da za su yi da Leeds yayin da ita kuma take neman tabbatar da cewa ba ta fita daga gasar Firimiya ba.
Bayan Manchester City, Leeds za ta kara da Newcastle wadda ke ta uku a teburin Firimiya da maki 65. Tun da Newcastle na neman tabbatar da cewa ta shiga gasar Zakarun Turai ba za ta so ta barar da maki ba.
Yaran Sam za su kara da West Ham da kuma Tottenham, wadanda a kakar bara suka taka rawar gani amma suna fuskantar matsala a wannnan lokacin.
Ganin irin kungiyoyin da Leeds za ta kara da su na sa wasu na ganin zai yi wuya ta iya tsira.
Sai dai Sam na ganin Leeds za ta iya kai labari.
Alladyce ya ce ya san zai sha wahala sosai wajen gudanar da Leeds United "amma na fuskanci wahalhalu da yawa a baya kuma ban karaya ba."
"Na so na samu lokaci mai yawa don tafiyar da kungiyar, amma muna da wasanni hudu kawai kuma ina fatan zai iya tabbatar da wannan kuniyar cikin gasar Firimiya."