Mikel Arteta na ganin 'yan Arsenal ne da laifi wajen barar da maki a wasansu da West Ham/Photo: Reuters

Wannan ita ce tambayar da mutane ke yi bayan Arsenal, wadda ke kan gaba wajen samun maki a gasar Firimiya, ta yasar da maki hudu cikin wasanni biyu a makonni biyun da suka wuce.

A karawarta da Liverpool, Asernal ta zubar da maki biyu bayan sun tashi 2-2, lamarin da ya rage ratar da ta bai wa Man City, mai bin ta a teburin Firimiya zuwa shida.

Arsenal ta sake maimaita wannan koma-bayan a lokacin da ta barar da maki biyu a wasan da ta buga da West Ham inda suka tashi da 2-2, lamarin da ya mayar da ratar da ke tsakaninta da Man City maki hudu.

Bugu da kari, Man City na dakon wasa daya da ba ta yi ba. Idan ta yi nasara a wasan, makin da ke tsakaninta da Arsenal zai koma daya tilo.

Wannan zai saka Arsenal a wani yanayi mai hatsari saboda idan ta sake irin wannan barin makin, za ta iya rasa matsayinta na kasancewa ta daya a saman teburin Firimiya.

Kocin Man City, Pep Guardiola ya ce kungiyarsa na bukatar nasara in har tana son ta lashe gasar Firimiya/Photo:Reuters

Kocin Arsernal, Mikel Arteta, yana ganin dole su sauya tunani idan har suna son su dauki kofin Gasar Firimiya.

“Dole mu dora wa kanmu laifin yadda muka tsare gidanmu,” in ji Arteta a lokacin da yake magana da manema labarain bayan karawarsu da West Ham ranar Lahadi.

Ya ce abin da Arsernal take da iko a kai a halin yanzu shi ne inganta salon wasanta ta yadda za ta iya ci gaba da yin nasara.

Man City na "bukatar nasara"

Ranar Laraba 26 ga watan Afrilu Manchester City za ta karbi bakuncin Arsenal a gasar Firimiya, kuma tuni kocin City, Pep Guardiola, ya fara cewa dole kungiyarsa ta yi nasara kan Arsernal.

“Kamar yadda na fada a tarukan maneman labarai na baya, nasara, nasara da nasara muke bukata,” a cewar Pep Guardiola a lokacin da yake magana da manema labarai.

A halin yanzu Arsenal ba ta sha kaye ba cikin wasanni tara tun bayan da Man City ta doke ta a gida da 3-1.

Erling Haaland, madugun Manchester City, ya kafa tarihi a matsayin dan wasan da ya fara zura kwallaye 45 a raga a shekararsa ta farko a wani kulob din gasar Firimiya/Photo:Reuters

Idan Man City ta iya doke ta a karawar da za su yi a Etihad ranar Laraba ta sama, Arsenal za ta fada cikin mawuyacin hali wanda zai yi wuya ta iya fita daga matsalar idan har Man City ba ta barar da maki ba.

Idan kuwa Arsenal ta dauki fansa kan Man City, za ta samu ta karfafa matsayinta a saman teburin gasar Firimiya wanda ka iya kai ta ga lashe kofin gasar Firimiya.

Ranar 28 ga watan Mayu ne dai za a gama gasar Firimiya ranar da Arsenal za ta karbi bakuncin Wolves, ita kuwa Man City za ta je gidan Brentford wasa.

Sanin wanda zai dauki kofin gasar Firimiya na wasan bana ka iya kai wa ranar 28 ga watan Mayun.

TRT Afrika da abokan hulda