#KKM52 : Jim Ratcliffe's Ineos declares interest in buying Man Utd / Photo: AFP

Wani biloniya dan kasar Qatar, Sheikh Jassim ya aika tayi karo na biyu don sayen babban kulob din kwallon kafa na Ingila, wato Manchester United.

Gidajen jaridun Burtaniya sun ba da rahoton cewa kulob din na Manchester United ya sami tayin na biyu daga dan Qatar mai niyyar siyan hamshakin kulob din.

Gidan jarida na Press Association da kuma Guardian, da ma wasu daban, sun sanar ranar Asabar cewa Sheikh Jassim Bin Hamad Bin Jassim Bin Jaber AI Thani, wanda shugaban bankin Qatar Islamic Bank ne ya ba da tayin a karo na biyu.

Biloniya dan Burtaniya Jim Ratcliffe ya turo sabon tayi ranar Alhamis, yayin da dan kasuwa Thomas Zilliacus ya shiga takarar neman sayen kulob din da ke da hedikwata a Old Trafford.

A baya an sanar da masu neman sayen kulob din cewa suna da har zuwa karfe tara na daren Laraba don su mika tayinsu. Amma yanzu ana cewa an kara wa’adin.

Ba a ambaci yawan kudin tayin ba, amma an fahimci cewa daya ko biyu cikin farashin yana wuraren fam miliyan 4.5 (dala biliyan 5.5).

Da farko Sky Sports News sun ruwaito cewa tayin na Sheikh Jassim an yi amanna ya kai kusan fam biliyan biyar (dala biliyan 12). Amma rahotannin da suka wallafa a shafinsu na intanet bai ambata adadin kudin ba.

Wannan zai mayar da kulob din Manchester United, wanda bai ci kofin firimiya ba tsawon shekara 10 ya zama shi ne kulob mafi tsada a tarihi.

Sai dai adadin ya gaza adadin Fam biliyan shida da aka ruwaito cewa Amurkawan da suka mallaki kulob din, sun masa kudi, wato dangin Glazers.

Sheikh Jassim da kuma Ratcliffe, wanda ya kafa kamfanin sinadarai na INEOS, shi ne a kan gaba cikin masu neman siyan matukar dangi Glazers suka saki mallakar kulob din.

A halin yanzu, attajirin kasar Finland, wato Zilliacus ya shiga takarar ranar Alhamis, inda ya mika tayin da y ace zai bai wa masoya kulob din damar mallakar kashi 50 cikin 100 na kulob din.

“Tayi na a ginu ne kan daidaito da masoya kulob”, a ta bakin Zilliacus, wanda ya kirkiri kamfanin salula na Future Works, cikin wata sanarwa.

Dangin Glazers sun bata ran da yawa daga masoya kulob din Manchester United, sakamakon dora wa kulob din dimbin bashi tun sanda suka saye shi a shekarar 2005.

Sun nuna shirinsu na cin gagarumar ribar kasuwancin nasu, yayin da suka nemi zuba jari daga masu sha’awar saya tun a Nuwamba.

Sai dai kuma, har yanzu za su iya fasa zabar sayar da kason mallakar kulob din, yayin da sauran masu jari a kulob din aka fahimci sun zabi zama marasa rinjayen mallaka.

A rahoton mujallar The Times, kamfanin zuba jari na Elliot Investment Management, wanda ya sayar da kulob din AC Milan kan kudi biliyan 1.3 a shekarar da ta gabata, shi ma ya mika tayinsa na sayen karamin jari a kulob din.

‘Kazamin farashi’

Sheikh Jassim yana neman sayen kashi 100 na mallakar kulob din, yana mai burin mayar da kulob din zuwa matayinsa “mai kima”.

Wata majiya ta kusa da tayin Sheik Jassim a baya ya labarta wa AFP cewa yana da kwarin gwiwa cewa tayin shi ne “mafi kyawu ga kulob din, da masoyansa, da kuma mutanen yankin” Manchester.

Shi kuwa Ratcliffe wanda masoyin kulob din ne tun yarinta, yana neman sayen gamammen hannun jarin dangin Glazers ne na kaso 69 cikin 100.

Attajirin mai shekaru 70 ya fada wa jaridar Wall Street Journal a wannan satin cewa bai shirya biyan “kazamin farashi ba” kan kulob din da ke jerin mafiya shahara a duniya.

Shi kuwa Ratcliffe, wanda a yanzu ya mallaki kulob din Nice da ke Faransa, ya ce burinsa na sayen Manchester United whi ne “kawai don cin kofuna”. Ya kira kulob din a matsayin “kadarar al’umma”.

TRT World