Ɗan wasan tsakiya na Manchester City, Rodrigo Hernandez Cascante ya ce Arsenal ta gaza lashe kofin gasar Firimiya ne saboda sun buga wasansu da Man City da "zuciya mara ƙarfi.''
Da yake magana da Optus Sport, Rodri ya ce: "A ƙashin gaskiya, ina ganin a nan abin yake [ya yi nuni da ƙoƙon kansa]. Abin a zuciya yake. [Akwai] gwarazan 'yan wasa a gasar nan, akwai su a duka ƙungiyoyin.
"Ya cancanci Arsenal [ta ci gasar], sun yi matuƙar bajinta a wannan kakar, amma ina ganin bambancin yana nan [ya sake nuni da kansa].
"Lokacin da suka zo nan, sun fuskance mu a Etihad, da na gan su sai na ce: 'Ah, ga mutanen nan, ba so suke su doke mu ba, suna neman kunnen-doki ne kawai.' Kuma ina ganin da irin wannan zuciya muke da ita a Man City, da mu ma mun yi abin da suka yi.
"Kuma haka muka tarfa su. A ƙarshe, idan ka ba mu maki guda, za mu ci wasannin ƙarshe bakwai, ko takwas duk da hakan da wahala matuƙa. Don haka nake ganin [lashe gasar] tana da alaƙa da ƙarfin zuciya."
Kofi na huɗu a jere
Manchester City ta lashe kofin gasar Firimiya na huɗu a jere, inda ta zamo ƙungiya ta farko a gasar Firimiya da ta taɓa cin kofi huɗu a jere.
Tawagar ƙarƙashin Pep Guardiola, ta doke West Ham United da ci 3-1 a wasansu na ƙarshe a wannan kaka a filin Etihad, inda da shi ne suka lashe kofin, wanda Arsenal da ke mataki na biyu take hanƙoron lashewa.
A yanzu Man City ta kammala kakar 2023/24 da maki 91, wato maki biyu sama da na Arsenal, kuma har yanzu za su iya lashe gasar FA a wasan ƙarshe tare da maƙwabtansu Manchester United a filin wasa na Wembley ranar Asabar 25 ga Mayu.