Bayan gaza samun tayin sayar da 'yan wasanta uku, Ronald Araujo, Frenkie de Jong, da Ansu Fati, a yanzu ƙungiyar Barcelona ta Sifaniya ta ƙuduri aniyar sayar da gwarzon ɗan wasanta Ilkay Gundogan.
Rahotanni sun nuna cewa Barca ta shirya sayar da haziƙin ɗan wasan a bazarar nan, yayin da ake sa ran ƙungiyoyi daga Saudiyya da Qatar za su yi tayin sayan sa.
Ƙungiyar Barcelona tana fama da matsin tattalin arziƙi, inda hakan ya hana ta damar sayo manyan 'yan wasa a kakar bara.
Duk da lamura sun fara daidaituwa cikin watanni 12 na baya, gabanin fara kakar baɗi, Barcelona na neman hanyar sayo taurarin 'yan wasa masu tashe daga tawagar Sifaniya, wato Nico Williams da Dani Olmo.
Kafin iya sayon 'yan wasan da ake sa ran za su ci kuɗi har Euro miliyan 100 ($108.5m), Barcelona ta yi tunanin sayar da Ronald Araujo, Frenkie de Jong da Ansu Fati.
Sai dai 'yan wasan uku suna fama da jinya, inda biyu cikinsu aka cire tsammanin dawowarsu filin wasa har sai ƙarshen 2024. Wannan ya tilasta wa Barca fara shirin sayar da Gundogan, kamar yadda rahotannin suka nuna.
A halin yanzu dai, ƙungiyar Qatar ta Al Sadd, da kuma wata ƙungiya da ba a ambato sunanta ba a Saudiyya, su ne kan gaba wajen neman sayan Gundogan.
A bara ne Barcelona ta sayo Ilkay Gundogan daga Manchester City, inda kwantiraginsa ba za ta ƙare ba har sai bazarar 2025.