Gwarzon ɗan wasan tennis ɗan Sifaniya, Rafael Nadal ya bayyana ranar Alhamis cewa zai yi ritaya daga buga wasan tennis yana da shekaru 38, bayan an kammala gasar Davis Cup ta watan gobe.
Rafael Nadal ya lashe manyan kofunan Grand Slam 22 shi kaɗai a tsawon rayuwarsa ta wasa wadda ke cike da ban mamaki, inda ya yi hamayya da manyan 'yan tennis biyu, wanda da su ake kira Gawurtattu Uku, wato Roger Federer da Novak Djokovic.
Salon wasa irin na Nadal inda yake wasa tamkar ransa zai fita, ya sanya shi cikin jaruman filin wasa na taɓo, inda a nan ne ya lashe kofuna 14 a gasar French Open.
“Tabbas, duk abin da na samu tamkar mafarki ne ya zamo gaskiya," Nadal ya faɗa a wata sanarwa a shafin sada zumunta. "Zan bar wasa ina mai cike da jin daɗi a raina, bayan nuna bajintata, da nuna ƙoƙari ta kowace hanya”.
Gwarzon ɗan wasan ya nuna cewa matakin da ya ɗauka yana da alaƙa da yawan raunin da yake samu.
“Gaskiyar lamarin shi ne na shafe shekaru ina wahala, musamman shekaru biyu na baya-bayan nan. Ba na jin na buga wasa ba tare da wata matsala ba. Tabbas wannan mataki ne mai tsauri, wanda ya ɗauke ni tsawon lokaci. Amma a wannan rayuwa, komai yana da farko da ƙarshe,” in ji Nadal.
Sarki a filin taɓo
Tarihin da ya kafa ya zarta na duk wani namiji ko mace, da ya ci a gasa guda cikin manyan gasanni tennis huɗu na duniya. Wannan fice ya sa an girmama Nadal da butum-butumi wanda aka ajiye dab da ƙofar shiga filin Roland Garros kusa da filin wasan tennis na Court Philippe Chatrier.
Nadal ya ce yana farin cikin kammala wasansa a gasar Davis Cup, wadda za ta gudana a garin Malaga, na Sifaniya.