Omar Marmoush ɗan asalin Masar ne mai shekara 25. / Hoto: Manchester City

Manchester City ta sanar da cewa Omar Marmoush ya shigo ƙungiyar daga Eintracht Frankfurt ta Jamus, bayan sanya hannu a kwantiragi zuwa 2029.

Manchester City ta zuba tsabar kuɗi har euro miliyan €75 don ɗauko ɗan wasan tsakiyan, wanda ya zama ɗan wasa na uku da Pep Guardiola ya jagoranci City wajen ɗaukowa a Janairun nan.

Kwantiragin da Marmoush ya sanya wa hannu ta shekara huɗu da rabi ce, inda ya baro ƙungiyarsa ta Eintracht da ke wasa a gasar Bundesliga, bayan ya ci ƙwallaye 37 da tallafin ƙwallo 20 a wasanni 67.

Marmoush zai ƙara wa City yawan 'yan wasan gaba, yayin da take fama da rashin tagomashi. A Larabar nan City ta gamu da rashin sa'a inda PSG ta doke ta da ci 4-2 a gasar Zakarun Turai.

Lamba 7

Sabon ɗan wasan zai saka riga mai lamba 7, kuma ya faɗa yayin gabatar da shi a sabuwar ƙungiyar tasa cewa, "Wannan rana ce da ba zan taɓa mantawa da ita ba."

"A ce ka samu shiga Manchester City, ɗaya cikin ƙungiyoyi mafi kyau a duniya abu ne mai ƙayatarwa. Ina farin ciki... Ina fatan fara aiki da haɗuwa da sauran 'yan wasa da kuma nuna wa masoya Manchester City ƙoƙarina.”

Daraktan wasanni na Man City, Txiki Begiristain ya ce, “Omar haziƙin ɗan wasan gaba ne, kuma ina alfaharin cewa ya zo ƙungiyarmu.”

A yanzu dai, Manchester City za ta yi fatan farfaɗowa a wasanta na gaba da Chelsea ranar Asabar a gasar Firimiya, kafin daga baya ta kara da Club Brugge a wasan ƙarshe na rukuni a gasar Zakarun Turai.

TRT Afrika