Lamura suna ci gaba da lalacewa a Manchester City bayan da ƙungiyar ta sha da ƙyar a hannun Everton, inda suka tashi wasa yau Alhamis da ci 1-1, a Gasar Firimiya.
Wani abu da ya ja hankalin masoya Man City shi ne yadda gwarzon ɗan wasa Erling Haaland ya zubar da bugun ɗurme, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, ƙwallon da aka yi fatan ta bai wa ƙungiyar nasara.
Zubar da fenareti ya ƙara sanyaya gwiwar koci da 'yan wasan City, inda da jiɓin goshi suka ƙarasa wasan da aka buga a filin wasansu na Etihad.
A minti na 53 ne golan Everton Jordan Pickford ya kaɗe ƙwallon da Haaland ya buga a yadi na 18.
Tun da fari, City ta ci ƙwallo a minti na 14 ta hannun Bernardo Silva, kafin Iliman Ndiaye na Everton ya farke a minti na 36.
Duk da cewa Man City ce ke riƙe da kofin Firimiya na bara, ƙungiyar na ci gaba da rasa tagomashi da gwarjini a duniyar ƙwallon, inda ake jajanta makomar kocinsu mai tarihin nasarori, Pep Guardiola.
Dabara ta fara ƙare wa Guardiola
A yanzu dai City ta rasa maki biyu cikin uku da ya kamata ta samu bayan buga wasa da ƙaramar ƙungiyar da ke mataki na 15.
Wasan na yau ya bar City a mataki na 7 a teburin Firimiya.
Zuwa yanzu a kakar wasa ta 2024-25 a Firimiya, Man City ta gaza cin rabin wasanninta bayan buga jimillar wasanni 18.
Kuma wannan shi ne wasa na uku da suka gaza yin nasara a jere.
Gabanin wasan na Alhamis, rahotanni sun ce 'yan wasan City sun kwashe daren Kirsimeti a filin wasan da suke atisayen don ƙara kuzari da kyautata damarsu ta yin nasara.
Koci Pep Guardiola ya hana 'yan wasan nasa komawa gidajensu, inda ya tilasta musu kwana a ɗakunan kwana na filin wasansu a daren Laraba.
Ganin yadda ƙungiyar take ta shan kashi a hannun manya da ƙananan ƙungiyoyi, a yanzu ƙungiyar ta ƙara shiga tasku, inda ta ƙagu ta sauya alƙibla zuwa cin nasara a wasannin da ke gaba.