Rahotanni sun ambato jaridar The Times ta Ingila, tana cewa ƙungiyar Manchester City ta gabatar da ƙara kan zargin taka doka da hukumar gasar Firimiya ke yi, game da batun kimanta kuɗaɗen da kamfanoni ke biyan kulob don ɗaukar nauyi.
Ƙarƙashin dokar da hukumar ta fito da ita a 2021, lokacin da kamfanin zuba jari na Saudiyya ya sayi kulob ɗin Newcastle, duka yarjejeniyar kuɗi tsakanin kulob da kamfanonin da ke da alaƙa da mamallaka kulob, dole sai an tantance su a killace, don fayyace ƙimarsu ta kasuwanci.
Man City tana iƙirarin cewa dokar mai sa-ido kan hada-hadar kuɗi ba ta kan ƙa'ida, kuma ba ta dace da dokokin Birtaniya ba. Haka ne ya sa suke yunƙurin kawo ƙarshen aiki da dokokin da ke da suna Associated Party Transaction (ATP).
Bayan nan kuma, Man City na neman diyya kan asarar kuɗin da suka tafka sakamakon aiki da dokar.
A ƙarar da ta shigar cikin daftari mai shafuka 165, City ta yi iƙirarin cewa dokar na nuna musu "wariya". Za a yi zaman kotu kan ƙarar tsawon sati biyu da za a fara daga Litinin 10 ga Yuni.
Sai dai kuma tun a watan Fabrairun 2023, hukumar ta Firimiya ta kai Manchester City ƙara kan taka dokokin hada-hadar kuɗi har sau 100, cikin shekaru tara, wanda ya fara daga 2009 zuwa 2018.
Zargin da hukumar ke yi wa City shi ne cewa, kulob ɗin bai bayar da cikakkun bayanai kan jimillar kuɗin da suke biyan kocinsu ba, tsawon shekaru huɗu, wanda hakan ke nuna zargin biyan koci kuɗi a ɓoye sama da yadda suka bayyana a hukumance.
Amma sai a watan Nuwamba ne za a yi shari'ar zarge-zarge 115 da hukumar Firimiya ta yi kan Manchester City.