Bayan badaƙalar gaza rijistar ɗan wasan da Barcelona ta sayo tun a bazarar bara, wato Dani Olmo, wata ƙungiyar masoya kulob ɗin sun harzuƙa, sun fitar da rai daga shugabancin ƙungiyar.
Ƙungiyar magoya bayan Barcelona mai suna 'Som un Clam' sun fitar da wata wasiƙa mai neman da shugaban ƙungiyar Joan Laporta da kwamitin gudanarwar ƙungiyar su ajiye aikinsu sakamakon batun Dani Olmo.
Wasiƙar ta yi kakkausar suka kan Laporta inda ta zarge shi da ci gaba da nuna halayyar 'ƙarya da yaudara', sannan suka nemi ya yi murabus.
Shugabannin Barcelona sun yi ƙaurin suna a baya bayan nan tun bayan da Shugaba Laporta ya karɓi aiki a Maris ɗin 2021, daga tsohon shugaban ƙungiyar Josep Maria Bartomeu.
An kawar da tsohon shugaban ne bayan gudanar da zaɓe sakamakon saka ƙungiyar a cikin matsalolin kuɗi da wasu tarin matsaloli.
Sai dai sabon shugaban, Laporta ya yi ta fama wajen farfaɗo da ƙungiyar da cika alƙawuran ceto ta da ya yi.
Sayan Olmo da Victor
Babbar matsalar baya bayan nan da ƙungiyar ta faɗa ita ce ta sayo 'yan wasa biyu a kakar bara, Dani Olmo da Pau Victor, waɗanda aka gaza musu rijistar buga wasa a ƙungiyar tun lokacin.
Shugaban ƙungiyar masoya Barcelona, Joan Camprubi Montal ya bayyana ra'ayinsa kan matsalar da 'Laporta ya jefa su', kuma ya nemi shugaban da kuma kwamitin gudanarwarsu su ajiye aiki.
A yanzu alamu na nuna cewa 'yan wasan biyu ba za su buga wa kulob ɗin wasa ba a rabin kakar bana da za a buga wannan shekara.
Kuma magoya bayan ƙungiyar na ganin wannan abin kunya ne cikin jerin abin kunyar da ke faruwa a ƙungiyar tasu.
Duk da ɗan wasan Dani Olmo ya bayyana aniyarsa ta cigaba da jiran tsammani a Barcelona, a cewar wakilinsa, zai janyo wa ƙungiyar asarar kuɗin da ya kai dala miliyan 343.
Sai dai har yanzu Barca na fatan samun damar yin rijistar 'yan wasan bayan ta amince da wani shiri na sayar da tikitin jerin wuraren zama na alfarma a filin wasansu na Camp Nou, domin samun kuɗi.