Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana Liverpool a matsayin mai wuyar sha’ani bayan kungiyar ta rike su da ci 2-2.
“Idan ka lura da abin ba suka yi wa manyan kungiyoyi har a wannan kakar, kungiya ce ingatacciya. Da wahala ka rinjaye ta har na minti 90,” in ji Arteta a bayanin da ya yi bayan wasa tsakanin Liverpool da Arsenal.
“Akwai lokacin da za su sauya yadda wasan ke tafiya zuwa yadda suke so ya kasance. Da zarar sun kai wasan wancan matakin, kungiyoyi kalilan ne za su iya ja da su,” a cewar Arteta.
Minti 28 da fara wasa ne dai Arsenal ta zura kwallo biyu a ragar Liverpool, sai dai Mohamed Salah ya farke wa Liverpool kwallo daya minti 42 da fara wasa.
Mohamed Salah din ya sake samun damar farke wa Liverpool kwallo ta biyun minti 54 da fara wasa ta hanyar fenareti, sai dai ya barar da fenaretin.
Sai dai a minti na 87 Roberto Firminho ya zura kwallo a ragar Arsenal, lamarin da ya hana ‘yan Gunners samun maki uku.
Sakamakon ya nuna cewa Arsenal tana saman teburin gasar Firimiya da maki 73, kuma Manchester City na biye da ita da maki 67 da wasa daya da ya rage mata.
A yanzu a iya cewa kungiyar Arsenal ko kungiyar Manchester City ne ke da damar iya lashe gasar Firimiya ta kakar bana.