Yayin da ake raɗe-raɗin cewa ɗan wasan Bayern Munich, Leroy Sane na shirin komawa Arsenal ko Manchester United a Ingila, ɗan wasan ya musanta hakan, kuma ya ce yana jin daɗin zamansa a Jamus.
Sai dai Sane ya amsa cewa gasar Firimiya ta Ingila har yanzu tana burge shi, kasancewa ya taɓa buga wa Manchester City a baya.
A 2016 ne Sane ya bar Schalke 04 ta Jamus inda ya shiga tawagar Man City ƙarƙashin Pep Guardiola, kuma ya lashe kofin Firmiya har sau uku. Amma gabanin kakar 2020-21, ya koma Jamus inda ya shiga Bayern Munich.
Ɗan wasan wanda ɗan asalin Jamus ne yana da kwantiragi da Bayern wadda ba za ta ƙare ba sai a ƙarshen 2024-25. Amma har zuwa yanzu bai sanya hannu kan sabuwar kwantiragi ba.
Wannan ne ya sa ake tunanin zai bar ƙungiyarsa ta Bayern, har ake hasashen zai koma Ingila inda zai shiga Arsenal ko Manchester United, ko kuma Newcastle.
Kallon Firimiya
Sane mai shekaru 28, ya musanta raɗe-raɗin cewa yana shirin komawa Ingila, amma ya ce tabbas har yanzu shi mai sha'awar gasar Firimiya ne.
Shafin Goal ya ambato Sane yana faɗa wa mujallar SportBild cewa, "Ina sha'awar gasar ta Firimiya, har yanzu ina kallon wasu wasanni a talabijin. Amma hankalina yana kulob ɗin da nake iya nuna bajintata, kuma nake lashe kofuna."
"Ina samun wannan a FC Bayern. A nan ne nake da mafi girman abin da nake muradi kuma nake cin ƙwallaye", in ji Sane.
Ranar Talatar da ta gabata Sane ya buga wa tawagar ƙasarsa Jamus a wasansu na ƙarshe a gasar Nations League matakin rukuni, inda suka kara da Hungary aka tashi da ci 1-1.
A yanzu Sane zai mayar da hankalinsa zuwa ƙungiyarsa ta Bayern, wadda za ta buga wasa da Augsburg a gasar Bundesliga ranar Juma'a.