Wasannin da suka gudana a ƙarshen makon jiya a wasu manya-manyan gasannin ƙwallo na Turai da Amurka, sun janyo suka kan hukuncin da alƙalan wasa ke zartarwa yayin wasa, wanda ke haifar da zalunci kan wasu ƙungiyoyi ko 'yan wasa.
Daga cikin wasannin da aka samu taƙaddama kan hukunce-hukuncen alƙalai, akwai wasan Real Madrid da Espanyol a Sifaniya, da wasan Manchester City da Arsenal, da na Liverpool da Bournemouth a Ingila, da kuma na Inter Miami da New York City a Amurka.
Real Madrid da Enpanyol
Wasan mako na shida na gasar LaLiga tsakanin Real Madrid da Espanyol, wanda Madrid ta lashe da ci 4-1 ya janyo cecekuce bisa hukuncin da alƙalin wasan ya yi na bai wa Madrid bugun ɗurme a minti na 90 na wasan.
An ruwaito kocin Espanyol, Manolo Gonzalez yana caccakar hukuncin bai wa Real Madrid bugun da suka zura ƙwallo ta huɗu, inda ya ce batun “Ya ƙona min rai”.
Espanyol wadda ke mataki na 13 a teburin LaLiga, ta yi iya ƙoƙarinta a filin wasan Madrid a wasan na Asabar, inda ta fara zura ƙwallon farko sakamakon kuskuren golan Madrid Thibaut Courtois, amma duk da haka wasan ya ƙare da rashin nasara da ci 4-1.
Manolo Gonzalez ya bayyana cewa an tafka kurakurai a wasan da dama, waɗanda suka haifar da rashin nasarar ƙungiyar tasa. Ya mayar da hankali kan batun kayar da ɗan wasan Madrid, Endrick Felipe, wanda ɗan wasan Espanyol Carlos Romero ya yi.
Kamar yadda aka yi ta nunawa a hotuna da bidiyon abin da ya faru bayan wasan, kocin Espanyol ya ce an kayar da Endrick ne a wajen da'irar 18, wanda ke nufin babu bugun ɗurme.
Gonzalez ya ce “Tabbas a wajen da'ira ne. Na sake kallon abin da ya faru lokacin da Endrick ya zube, ƙafafunsa na wajen da'ira". Sai dai alƙalin wasan ya ba da uzurin cewa "An ci gaba da riƙe Endrick har cikin da'irar.”
Arsenal da Manchester City
Mikel Arteta, kocin Arsenal ya soki hukuncin korar ɗan wasansa Leandro Trossard da aka yi yayin wasansu da Manchester City a yammacin Lahadi 20 ga Satumba a gasar Firimiya, inda aka tashi wasan da ci 2-2.
Wasan da ɗan wasan Manchester City John Stones ya farke ƙwallo a minti na 97, ya bai wa City damar samun maki guda a takarsu da Arsenal, wadda ta ba su damar yin canjaras, abin da ya sa Arsenal ta gaza kamo su a teburin maki na Firimiya.
Arsenal ta yi zaton ta lashe wasan bayan da aka tafi hutun rabin lokaci tana da ci 2-1 kan City, bayan da Riccardo Calafiori da Gabriel Magalhaes suka ciyo mata ƙwallaye biyu, waɗanda suka wanke ƙwallon da Erling Haaland na City ya fara ci a minti na 9.
Abin da Arteta ya soki alƙalin wasan shi ne, yalon katin da aka bai wa Leandro Trossard a ƙarshen zagayen farko, hukuncin da ya sauya wasan gabaɗaya kasancewa Arsenal ta ƙare wasan da 'yan wasa 10.
Da aka tambayi Arteta kan korar Trossard saboda ya yi wancakali da ƙwallo bayan ya yi wa ɗan wasan Man City ƙeta, Arteta bai ji daɗin hukuncin ba, duk da dai bai fito ƙarara ya faɗa ba, Sai dai ya ce, “Ba aikina ba ne na zo na yi hukunci kan abin da ya faru".
Liverpool da Bournemouth
A ranar Asabar 21 ga Satumba, Liverpool ta doke Bournemouth da ci 3-0 a gasar Firimiya, inda alƙalin wasan Tony Harrington ya bai wa kocin Bournemouth yalon kati, wanda zai haramta masa jan ragamar ƙungiyar a wasansu na gaba a gasar.
Alƙalin wasan ya ladabtar da kocin Bournemouth, Andoni Iraola sakamakon haura da'irar filin wasa. Sai dai a bayaninsa bayan wasan, Iraola ya bayyana cewa 'rashin fahimta' aka samu tsakaninsa da rafalin wasa, har ta kai shi ga samun katin gargaɗin.
Shafin BBC ya ambato kocin yana cewa, "Ina neman a ba da hukuncin satar shiga ne.... Amma alƙalin ya ce min, ‘Bai kamata ka nemi yalon kati ba’.
Inter Miami da New York City
A ranar Asabar ne a gasar Major League ta Amurka, ƙungiyar Inter Miami ta yi canjaras da New York City da ci 1-1, bayan da NYC ya farke ƙwallo a ƙarin minti biyar na ƙarshen wasan, bayan Miami ta ci nata ƙwallon a minti na 75.
Sai dai kocin Miami, Tata Martino ya caccaki alƙalin da ya jagoranci wasan kasancewa an kayar da ɗan wasan Miami Yannick Bright a da'irar 18 ta gidan NYC, amma ba a ba Miami bugun ɗurme ba.
An buga wasan ne a gidan Yankee Stadium da ke birnin New York, kuma lokacin da ɗan wasan NYC, James Sands ya saka goshi ya ci ƙwallon da ta farke wasan, mai tsaron gida na NYC Thiago Martins ya ture ɗan wasan baya na Miami, Yannick Bright.
Sai dai duk da an duba abin da ya faru da fasahar alƙalanci ta VAR, alƙalin wasan ya amince da ƙwallon da aka ci, wanda kocin Miami ya kausasa ƙin amincewarsa da hukuncin, inda ya ce wasan "bai samu sahihin alƙali" ba, kuma ya kamata Miami ce ta lashe wasan.