A ranar Laraba wata kotu a Burtaniya ta yanke hukuncin cewa Manchester City ta biya tsohon ɗan wasanta, Benjamin Mendy, mafi yawan kason albashinsa da ba ta biya ba, wanda ya kai fam miliyan £11.5 (dala miliyan $15).
Ƙungiyar ta riƙe masa kuɗaɗen ne bayan wata ta zarge shi da yi mata fyaɗe da cin zarafinta tun a 2021.
Benjamin Mendy, ɗan wasan Manchester City ɗan asalin Faransa, wanda a baya yake ɗaukar albashin £500,000 duk wata a gasar Firimiya ta Ingila ya je kotun ƙwadago a watan jiya.
Mendy ya yi iƙirarin cewa wani babban jami'in ƙungiyar ya ba shi tabbacin cewa zai samu ƙuɗaɗen nasa da zarar an wanke shi daga zarge-zarge a kotu.
A watan Janairun 2023 ne kuto ta ce ba a same shi da laifi ba, kan zarge-zarge shida da suka haɗa da fyaɗe da zargi guda kan cin zarafi ba. Bayan sake shari'ar tasa an gaza samun sa da laifi guda na yi ko ƙoƙarin fyaɗe ba,
Ɗan wasan bayan ɗan shekara 30, wanda a yanzu yake buga wasa a ƙungiyar Lorient ta gasar Ligue 2 ta Faransa.
Kotun ƙwadago
Alƙali a kotun ƙwadago, Joanne Dunlop ta ce a yayin yanke hukuncin cewa ta kammala cewa Mendy "yana da haƙƙi samun wani kaso na jimillar basukan, amma ba duka ba."
Mendy ya kwashe kakar wasa biyu a tsare,wanda ke nufin kusan watanni biyar cikin watanni 22 sun shiga cikin zangon lokacin da yake iƙirari.
Alƙaliyar ta ce a hukucin nata cewa lokacin da Mendy ba ya tsare, yana "shirye kuma ya so ya" yi aiki.