Yayin da ya rage kusan wasanni 12 a kakar bana ta gasar ƙwallon ƙafar ƙwararru na yawancin ƙasashen Turai, rahotanni sun tabbatar da cewa koci guda uku za su bar kulob ɗin da suke jagoranta a ƙarshen kakar wasannin ta bana.
A Ingila, tun a watan Janairu ne kocin Liverpool Jorgen Klopp ya sanar da cewa a ƙarshen kakar bana zai bar kulob ɗin da ya kwashe shekaru tara yana jagoranta.
A karkashin Klopp, Liverpool ta lashe kofin Firimiya da kofin Zakarun Turai na UEFA, da kofin FA. Sannan ya ciyo wa Liverpool kofin UEFA Super Cup, da kofin FIFA Club World Cup.
Yayin sanar da aniyarsa ta barin Liverppol, Klopp ya bayyana cewa zai ɗauki hutun shekara guda daga aikin jagorancin kulob ɗin ƙwallo, sannan ba zai karɓi aikin jagorantar wani kulob ba a Gasar Firimiya ta Ingila.
A Sifaniya kuwa, Xavi Hernandez na Barcelona zai sauka daga muƙaminsa na manajan kulob din na Laliga da zarar ana kammala wasannin wannan kakar bana a watan Yuni mai zuwa.
Duk da cewa Xavi Hernandez ya ciyo wa Barcelona kofin LaLiga na bara, kocin wanda tsohon mashahurin dan wasan kulob din ne, ya sanar cewa yana ji kamar zai ajiye kwallon magwaro ne.
Xavi ya ƙara da cewa "Kullum ana sa mutum ya ji kamar ba ya yin kokari”, wannan ne ya sa yake farin cikin barin kulob din.
A kasar Jamus a gasar Bundesliga kuwa, Thomas Tuchel, wanda Bajamushe ne zai bar jagorancin kulob din Beyern Munich a karshen kakar bana, kamar yadda kulob din ya sanar a makon da ya gabata.
Tuchel ya ciyo wa Bayern kofin Bundesliga a bara, amma a wannan kakar labarin ba ya masa kyau. A yanzu Bayern tana da maki 53 ne kacal bayan buga wasanni 23, inda take bayan Bayer Leverkusen da maki 8.
Kocin Leverkusen dan kasar Sifaniya, Xabi Alonso, yana cikin manyan kocin da ake gani za su iya maye guraben da wadannan koci guda uku za su bari.
Shi dai Alonso ya fara zama koci da sa'a a ƙungiyar ta Leverkusen, inda zuwa yau ba a taba yin nasara kan kungiyarsa ba a kakar bana, cikin dukkanin gasanni.