Victor Osimhen zai bar Napoli a ƙarshen kakar bana, inda zai koma buga wasa a Ingila ko Faransa. / Photo: Reuters

Rahotanni sun nuna cewa Victor Osimhen, gwarzon ɗan wasan Afirka ɗan asalin Nijeriya, wanda ke buga wasa a Napoli ta Italiya ya yi watsi da tayin zuwa PSG, inda ya gwammace ya tafi Arsenal ko Chelsea.

Tun a Janairu ne Osimhen, mai shekaru 25, ya bayyana cewa ya "yanke hukunci kan mataki na gaba" a harkar wasanninsa. Inda aka yi ta yaɗa cewa zai koma ƙungiyar PSG ta Faransa.

Sai dai tun a wancen lokacin ma, toshon ɗan wasan Chelsea kuma ɗan Nijeriya John Mikel Obi, ya bayyana cewa zai shawo kan Osimhen ya tafi zuwa Chelsea a Ingila.

Zuwa yanzu, alamu duka sun nuna cewa a kakar wasa mai zuwa, Osimhen ya zaɓi buga wasa a gasar Firimiya ta Ingila, maimakon gasar League 1 ta Faransa, duk da a baya ya taɓa buga wa ƙungiyar Lille ta Faransar kafin tafiyarsa Napoli.

Duk da cewa ya rattaba hannu kan kwantiragin cigaba da wasa a kulob ɗinsa na Napoli a Disamban da ya gabata, shugaban ƙungiyar ta Napoli Aurelio De Laurentiis ya tabbatar da cewa Osimhen zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana.

Da ma a kwantiragin Osimhen da Napoli, akwai saɗarar da ta ce zai iya barin ƙungiyar kan kuɗin da zai kai dala miliyan $114, kuma hakan ne ya janyo jita-jitar cewa zai tafi PSG ta Faransa, ko Chelsea, ko Arsenal.

Yayin da ake dakon ganin ina Osimhen zai zaɓa a Ingila tsakanin Chelsea da Arsenal, an ruwaito cewa domin ƙarfafa damarta ta samun Osimhen, Chelsea ta shirya zuba maƙudan kuɗi, gami da bayar da fansar 'yan wasa ga Napoli don karɓo Osimhen.

Osimhen, wanda shi ne ɗan wasan da ya ci kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa a nahiyar Afirka ta bara, ya ci ƙwallaye 76 a wasanni 131 da ya buga wa Napoli, inda ya jagorance su wajen lashe gasar Serie A ta bara.

A yanzu dai, ko ina ya fi dacewa Victor Osimhen ya tafi tsakanin sansanin Old Trafford na Chelsea, da Emirates na Arsenal, makonni masu zuwa ne za su fayyace inda rana za ta faɗi da gwarzon ɗan wasan mai tashe.

TRT Afrika