Yayin da tawagar Manchester City ke fara wasanta na gasar Zakarun Turai a daren yau Laraba tare da Inter Milan, tauraron ɗan wasan gaba na ƙungiyar ɗan asalin Norway, Erling Haaland zai yi ƙoƙarin cin ƙwallaye iya ƙarfinsa.
Kasancewar a wannan karo gasar ta Turai da aka fara kakarta a daren Talata 17 ga Satumban 2024, ta sha bamban sakamakon sauyin da aka yi a fasalin gasar, ƙungoyoyi za su buga wasanni sama da yadda aka gani a baya.
Yawaitar wasanni da za a buga zai iya bai wa Haaland ƙarin damar cin ƙwallaye, inda zai iya doke tarihin bajintar da Cristiano Ronaldo ya kafa a gasar ta mafi yawan cin ƙwallaye.
Haaland zai shiga gasar ta Turai a bana a karo na shida yayin da yake kan ganiyarsa ta cin ƙwallaye, kasancewa a wasanni huɗu kacal da ya buga da Man City a gasar Firimiya, ya ci zunzurutun ƙwallaye har tara.
Erling Haaland dai ba baƙon cin ƙwallo ba ne a gasar ta Zakarun Turai, kasancewar wasansa na farko a gasar tare da Red Bull Salzburg, ya zura ƙwallaye uku rigis a ragar Genk, a kakar 2019/2020. A Salzburg ya ci jimillar ƙwallaye 8 a gasar.
Ƙwallo 41 a wasa 39
A jimillar wasannin da ya buga, Erling Haaland mai shekaru 24 ya ci ƙwallaye 41 a wassani 39, wanda hakan shi ma wani tarihi ne da ya kafa.
Wannan ya sa ake ganin za a kai ranar da zai kamo Ronaldo, wanda ya fi kowa yawan ƙwallaye a gasar, bayan cin ƙwallo 140 a wasanni 183.
A yanzu Haaland ya samu damar ƙarin wasanni 2 a kaka guda inda zai iya kamo Ronaldo har ya masa fintinkau.
Haaland ya ci ƙwallaye 10 a wasanni tara na rukuni a kaka biyu na farko da ya buga da Manchester City, kuma ya lashe kofin na Zakarun Turai a shekarar 2023.
Babban ƙalubalen da ke gaban Haaland shi ne ƙungiyarsa ta City za ta fuskanci manyan kulob kamar Juventus da Paris Saint-Germain, baya ga Sporting CP da Feyenoord.
Ƙananan ƙungiyoyi
Sai dai a wasansu da ƙananan ƙungiyoyi ne ake sa ran Haaland zai samu damar cin karensa ba babbaka. Kulob ɗn sun haɗa da Sparta Prague, Slovan Bratislava, da Club Brugge.
Ganin yadda Man City ke kan ganiyarta, ana sa ran za ta ƙare wasanninta na rukuni cikin ƙungiyoyi takwas na gaba-gaba, inda kai-tsaye za ta cancanci zarcewa rukunin 'yan 16.
Idan kuwa Man City ba ta samu kai wa wannan matsayi ba, har ta ƙare a mataki na tara zuwa na 24 a teburin gasar, za su buga wasan share fage hawa biyu, wanda zai ba wa Haaland damar ƙara yawan ƙwallayensa.