Gwarzon ɗan wasan gaba na Manchester City, Erling Haaland, ya mayar da martani ga ɗan wasan baya na Liverpool, Trent Alexander-Arnold bayan da ya yi musu gorin amfani da kuɗi wajen cim ma nasarori.
"Bai san ya ake cin kofuna uku a kaka ɗaya ba", in ji Haaland a wata keɓantacciyar hira da ya yi da Sky Sports gabanin gagarumin wasan gasar Firimiya na ranar Lahadi, tsakanin Manchester City da Liverpool.
A bara ne Haaland ya jagoranci Man City wajen cin kofuna uku a kaka ɗaya, bayan da suka ci kofin Zakarun Turai, da kofin Firimiya, da kuma kofin FA. Ita kuwa Liverpool tun 2001 rabonta da cin kofi uku a kaka guda.
Tun da fari, Trent Alexander-Arnold ya yi iƙirarin cewa, "Cin kofuna yana da matuƙar muhimmanci ga masoya Liverpool", ba kamar Man City da kuɗi suka yi amfani da shi wajen cim ma nasara ba.
Alexander-Anold ya faɗi haka ne a wata hira da FourFourTwo, inda ya ce tarin kuɗin da City ke da shi ya sanya cin kofi ba wani abin birgewa ba ne ga kulob ɗin, da ma masoyansa, idan aka kwatanta da Liverpool da masoyansa.
Za a buga wasan ne a gidan Liverpool da ke Anfield ranar Lahadi da maraice, a ci gaba da mako na 28 na gasar Firimiya ta Ingila, wanda zai rage wasanni 10 kacal a kammala gasar ta kakar bana.
Ana yi wa wasan mai zuwa kallon wanda zai fayyace jagorancin teburin Firimiya, kasancewar maki ɗaya ne ya raba tsakanin Liverpool da ke jagorancin teburin a yanzu da maki 63, inda Manchester City biye mata da maki 62.
Duk wanda aka ci galaba kansa a wasan, zai iya faɗowa mataki na uku a teburin, matuƙar Arsenal da ke mataki na uku da maki 61 a yanzu, ta ci wasanta na wannan makon.