Haaland ya je Manchester City daga Borussia Dortmund a 2022. / Hoto: Manchester City

Zakaran ɗan wasan gaba na Manchester City, Erling Haaland ya tsawaita kwantiraginsa da shekaru 10 a ƙungiyar, inda kuma ya ce ya zo zama daram.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Juma'a ta ce kwantiragin ta kai tsawon shekara 9.5 kuma za ta ƙare a shekarar 2034.

A Tsohuwar kwantiragin ɗan wasan mai shekaru 24 zai zauna a ƙungiyar ne zuwa Yunin 2027, kafin a yanzu ya ƙulla yarjejeniyar tsawaita zamansa.

Ɗan wasan ɗan asalin Norway ya zo City ne daga Borussia Dortmund a shekarar 2022, kuma zuwa yanzu ya zura ƙwallaye 111 a wasanni 126 da ya buga.

Haaland ya ce, "Ina matuƙar farin ciki da sanya hannu kan sabuwar kwantiragin kuma ina fatan kwashe tsawon lokaci a wannan gagarumar ƙungiya".

"Manchester City ƙungiya ce fitacciya, mai cike da mutane masu hazaƙa da kuma masoya, kuma waje ne da ke taimaka wa duk mai son nuna hazaƙa.

Daraktan wasa mai barin gado na Manchester City, Txiki Begiristain ya ce: "Kowa a ƙungiyar yana alfahari da cewa Erling ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi.

"Cewa ya amince ya zauna tsawon lokaci alama ce mai nuna sadaukarwamu gare shi a matsayin ɗan wasa, da kuma soyayyarsa ga ƙungiyarmu.

"Ya yi matuƙar tasiri zuwa yanzu zamansa a nan inda ya tallafa wajen kafa tarihi da kowa ke iya gani."

TRT Afrika