Ferran Torres zai zage datse a makon wassanin zakarun turai / Hoto: Reuters

Dan wasan Barcelona Ferran Torres ya fada a ranar Talata cewa zai zage dantse a muhimmin makon da ke tafe na Zakarun Sifaniya, wadanda ke rasa 'yan wasa da dama sakamakon rauni da suke ji, ciki har da Robert Lewandowski.

'Yan wasan Catalania za su kara da Shakhtar Donetsk a ranar Laraba a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, inda suke sa ran samun nasarar kai wa mataki na uku a wasanni uku na Turai kafin su iya karbar bakuncin abokan hamayyarsu Real Madrid a gasar farko ta La Liga Clasico a ranar Asabar.

Torres, wanda ya yi ta fafutukar samun takarda tun da ya koma Barca daga Manchester City a shekarar 2022, ya ce yana da yakinin zai iya samun nasarar taimakawa kungiyarsa a wannan mawuyacin yanayi da take ciki.

"Yan wasanmu da dama sun ji rauni, ina ga a shirye nake na dauki wannan matakin don yin gaba, ina da yaƙini kan hakan kuma na shiryawa abin da ka iya zuwa," Torres ya shaida manema labarai gabanin fafatawarsa da Shakhtar.

"Ba na buƙatar samun ƙarin ƙwarin gwiwa, wanda nake da shi ya wadatar -- amma akwai abubuwa da dama da ke bukatar a inganta su."

Reuters