United ta barar da maki uku a karawarta da Brighton yayin da Brighton ta zura kwallo a ragarta miniti 98 da fara wasa/Hoto:Reuters

Dan wasan Manchester United wanda kuskurensa ya sa aka bai wa Brighton bugun fenaretin da ya sa United ta sha kaye, Luke Shaw, ya ce dole su yi kokarin samun gurbi a gasar Zakarun Turai.

Da yake magana bayan Man U ta sha kashi a hannun Brighton, dan wasan ya ce ‘yan wasan United suna sane cewa ba su da wani zabi illa su samu gurbi a gasar Zakarun Turai.

“Idan ka dubi damarmakin da muka samar kafin a tafi hutun rabin lokaci a wasan, ya kamata a ce mun ji dadin wasan,” in ji Luke Shaw.

United tana ta hudu a teburin gasar Firimiya da maki 63, yayin da Liverpool take bin ta da maki 59.

Kocin Machester United ya ce dole yaransa su farfado a karawar da za su yi da West ham ranar Lahadi/Hoto:Reuters

Wadanda suka kasance na daya zuwa na hudu a karshen gasar Firimiya ne za su samu shiga gasar Zakarun Turai daga Ingila.

Duk da cewar United tana da kwantan wasa daya, wasu na ganin akwai yiwuwar Liverpool ta kwace damar zuwa gasar Zakarun Turai daga hannunta.

“Na ji takaicin kayen da muka sha musamman ma don a karshen wasan ne aka doke mu,” a cewar Erik ten Hag.

Kocin United Erik ten Hag ya ce yanzu ‘yan Red Devils za su mayar da hankali kan karawarsu da West Ham ranar Lahadi ne don samun nasara.

Kocin na Man U ya ce abin da ya kara ba shi takaici game da yadda kuskuren da ya sa Brighton ta doke United shi ne Luke Shaw din ya tafka kuskuren ya yi kokari wajen tsare gidan United a karawar.

“Muna da komai a hannunmu. Dole ka yi kokari don yin nasara a kowane wasa. Kuma kada ka yi kuskure, sannan ka samu maki. Dole mu farfado,” in ji Erik ten Hag.

TRT Afrika da abokan hulda