Barcelona ta sanar da raba gari da kocinta Xavi Hernandez, wata ɗaya bayan kocin ya janye ƙudurinsa na ajiye aikin horar da kulob ɗin, duk da a baya ya sanar da aniyarsa ta barin muƙaminsa a ƙarshen kakar bana.
Yayin da wasa ɗaya ya rage a kammala kakar gasar LaLiga ta bana, inda Real Madrid ta lashe kofin gasar, Barcelona za ta kammala kakar bana babu armashi, kasancewar ta ƙare ne a mataki na biyu.
A yau Juma'a ne kulob ɗin ya tabbatar wa da Xavi, wanda tsohon tauraron ɗan wasan tsakiya na Barcelona ne, cewa ba zai ci gaba da jagorantar kulob ɗin a kakar baɗi ba.
Sanarwar ta zo ne bayan tattaunawa tsakanin shugaban Barcelona, Joan Laporta, da Xavi, da kuma sauran manyan jami'an ƙungiyar a filin atisayen kulob ɗin.
Barcelona ta sanar cewa shugabansu Laporta “ya sanar da Xavi Hernández cewa ba zai ci gaba da zama babban kocin ƙungiyar ba a kakar 2024-25.”
A bara ne Xavi ya ciyo wa Barcelona kofin LaLiga, amma sai ƙungiyar ta fara tafiya da ƙyar inda ta ƙare babu kofi ko guda, a gida da Turai, sannan ta ƙare LaLiga a mataki na biyu da tazara mai rata tsakaninta da Real Madrid.
Rahotannin sun nuna cewa Shuagaba Laporta ya sauya shawara kan Xavi ne, bayan rashin jin daɗin kalaman da kocin ya yi ga 'yan jarida kwanan nan, inda ya ce saboda ƙarancin kuɗin da Barcelona ke fama da shi zai yi wahala ta iya gasa da Real Madrid da sauran manyan ƙungiyoyin Turai.
A yanzu dai rahotanni sun nuna cewa an cimma yarjejeniya tsakanin Barca da tsohon kocin Bayern Munich, Hansi Flick, don maye gurbin Xavi.
Hansi Fleck zai zo Barca ne kan kwantiragin shekaru biyu zuwa 2026, inda kocin zai kawo mataimaka guda biyu daga Jamus, waɗanda za su tallafa masa.
Hansi Flick ya jagoranci Bayern Munich wajen cin kofuna shida a 2020. Ya kuma jagoranci tawagar ƙasar Jamus a watan Satumban 2023, inda tun bayan nan bai karɓi wani aikin horar do kowane kulob ba.