Yayin da ya rage wasanni tara a kammala Gasar Laliga ta bana, Barcelona wadda ke jan ragamar gasar da maki 73, ta sake barar da maki 2, sakamakon yin duro da Getafe a wasansu na karshen makon jiya.
Gabanin wannan, hamshakin kulob din na Sifaniya ya yi kunnen doki da Girona, inda nan ma ba su zura kwallo ko daya ba.
Hakan ya ba da mamaki, don kuwa duka kulob din biyu, Getafe da Girona idan aka hada makinsu a Laliga bai kai na Barcelona ba.
A duka wasannin biyu na gasar Laliga, da wasan kafin nan, inda suka buga da Real Madrid a Gasar Copa del Rey, Barcelona ta gaza zura ko da kwallo daya.
A yanzu dai kulob din mai maki 73 daga wasanni 29, yana da tazarar maki 11 tsakaninsa da mai biye masa, Real Madrid mai maki 62.
Shin ‘yan wasan gaban Barcelona ne suka yi la’asar, ko kuwa dai sa’a ce ta kubuce musu a daidai goman karshe na gasar Laligar bana?
Yanzu ina mafita ga yaran na Koci Xavi Hernandez?
Barca kar ku yi barci
Tashar wasanni ta ESPN ta ruwaito Xavi yana gargadin ‘yan wasansa da ka da su yi barci, a ci gaba da fafatawar neman lashe Kofin Laliga a karo na 27 a bana.
Abin da ya fi janyo damuwa shi ne yadda ‘yan wasan gaba na Bercelona suka kasa wani katabus cikin wasansu uku na baya-bayan nan.
A wasansu da Getafe, sau uku kawai suka kai harin da ya tunkari ragar kishiyoyinsu, inda Raphinha da Alejandro Balde suka daki turken raga.
Abu na biyu shi ne, wasansu na gaba zai kasance ne da wani babban kulob din, wato Atletico Madrid wanda yake mataki na uku a teburin Laligar.
Wannan ne ya janyo Xavi yake gargadin ‘yan wasansa cewa ya kamata su tashi tsaye cikin hanzari.
Ya ce "Ba ma cikin yanayin da ya kamata wajen kokartawa da kuma sakamakon wasa. Muna da kyakkyawan tagomashi a kakar bana, don haka bai kyautu mu fara barci ba. Muna da muhimman wasanni a gabanmu.”
Cikin wasannin tara da ke gaban Barcelona, mafi hadari shi ne karawa da Atletico Madrid. Sai kuma Real Betis da Villareal, wadanda duka suke cikin kulob shida na kan gaba a teburin Laliga.
A wasan su da Getafe, dan wasan gaba Raphinha sau daya ya kai hari kan raga, sannan sau biyu ya yi bugun daf da raga, kuma sau daya kacal ya yi nasarar yanka cikin karo uku.
Amma a karshe, shi aka bai wa gwarzon wasa, wanda ke nuna ba wanda ya fi shi kokari a wasan.
Ko dawowar Messi ce za ta dinke gaban Barcelona?
A wasannin 29 da suka buga zuwa yanzu, kwallaye 9 kawai aka sha Barcelona. Idan an kwatanta da mai biye musu, Real Madrid ta sha kwallaye har 24.
Wannan ya nuna ‘yan wasan bayan kulob din a dinke suke tamau. Haka nan, mai tsaron ragarsu, Marc-Andre ter Stegen ya buga wasa 22 ba tare da an zura masa kwallo ko daya ba a kakar bana.
Hakan ne ya sa aka raja’a kan cewa matsalar da ke damun Barcelona a halin yanzu tana wajen ‘yan wasan gaba ne.
A yanzu dai, rahotanni sun fara karfi kan yiwuwar dawowar tsohon gwarzon dan wasan na Barcelona, Lionel Messi a kakar sayen ‘yan kwallo ta bazara wadda ke karatowa.
Jaridar Faransa ta Le Parisien ta ruwaito cewa an rufe tattaunawar yarjejiniyar tsawaita wa’adin Messi a kulob dinsa na PSG. Wannan ne ke karfafa fatan da ake na Messi ya dawo taka leda a Barcelona.
A halin yanzu dai, Barcelona dai tana da manyan ‘yan wasa irinsu Robert Lewandowski, da Alejandro Balde, da Jordi Alba, da Ansu Fati, da Ferran Torres, sai kuma Pedri da kuma Ousmane Dembele da suke hutun jinya.
Ko da aka nemi jin ko Xavi ya damu da kanfar cin kwallo daga gwarzon dan wasa Lewandowski, ya yi nuni da cewa har yau Lewandowski ne ya fi kowa kwallaye a Laliga, da kwallaye 17.
A yanzu dai, Barcelona ke a mataki na farko, Real Madrid tana na biyu, sai Atletico Madrid a na uku, sannan Real Sociedad a na hudu, da kuma Real Betis da ke mataki na biyar.