Wojciech Szczesny zai fasa ritaya da ya yi don ya karɓi aikin tsaron gida a Barcelona. / Hoto: Reuters

Shahararren mai tsaron gida Wojciech Szczesny, wanda ya taka leda a Arsenal da Juventus, wanda kuma ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa a makonnin baya, zai dawo taka leda idan Barcelona ta ba shi sabuwar kwantiragi.

Barcelona dai na neman ɗauko sabon mai tsaron gida ne bayan da babban mai tsaron gidanta, Marc-Andre ter Stegen ya samu rauni a gwiwa, wanda zai hana shi buga wasa don yin jinya ta tsawon lokaci.

An yi wa Stegen, wanda Bajamushe ne tiyata, kuma ana tsoron ba zai dawo buga ƙwallo ba tsawon kakar wasan bana ɗungurungun.

Barca na duba gwanayen tsare raga daban-daban, ciki har da Szczesny, wanda ɗan Poland ne mai shekaru 34, a cewar shafin Mundo Deportivo wanda Goal.com ya ambato.

Barcelona za ta iya kawo sabon gola kafin a buɗe kasuwar cinikayyar 'yan wasa a Janairu, amma sai dai idan za ta ɗauko ɗan wasan da ba shi da kwantiragi da wata ƙungiya, wanda hakan ya taƙaita zaɓin da take da shi.

Szczesny dai ƙwararren gola ne wanda ya yi aiki da Arsenal da Juventus a zamaninsa. Sannan ya buga wa ƙasarsa Poland wasa sau 84, ciki har da a gasar Euro 2024.

Kocin Barcelona, Hansi Flick ya yi magana kan yiwuwar kawo sabon mai tsaron gida a jawabinsa ga 'yan jarida sai dai ya ce, "A yanzu ba mu da matuƙar buƙatar hakan, kuma mun yi amanna da aikin Iñaki Pena."

Inaki Pena shi ne wanda zai maye gurbin Ter Stegen a yanzu. Kuma ya tsare raga a kakar bara inda aka zura masa ƙwallaye 32 a wasanni 17.