Masoya da 'yan wasan Manchester City suna cikin fargaba kan makomar kulob ɗin a shari'ar da ake farawa wannan watan. / Hoto: Reuters

Za a fara sauraron ƙarar da aka kai Manchester City kan zarge-zarge 115 da hukumar Gasar Firimiya ke mata, na karya dokokinta kan hada-hadar kuɗi.

Tun a ranar 6 ga Fabrairun 2023 ne aka fara gabatar da zarge-zarge kan Manchester City, inda a yanzu bayan watanni 18, ake fara zaman sauraron ƙarar a ranar Litinin.

Waɗannan tuhume-tuhume 115 suna barazanar watsa wa Man City ƙasa a cikin abinci, inda ake tsoron za su disashe tagomashin ƙungiyar, tun bayan bayyanar batun wannan shari'a.

Haka nan ana tsoron wannan shari'a kan City wanda su ne zakarun gasar Firimiya, za ta ja lokaci inda za a gabatar da hujjojin da za su iya ɗaukar makonni 10 masu zuwa.

Hukumar ta Firimiya ta kai Manchester City ƙara kan taka dokokin hada-hadar kuɗi har sau 100, cikin shekaru tara, wanda ya fara daga 2009 zuwa 2018.

Ana fargabar cewa idan aka samu Man City da manyan laifuka, za ta iya fuskantar barazanar kora daga buga gasar Firimiya ɗngurungun.

Zarge-zarge 115

Zargin da hukumar ke yi wa City shi ne cewa, kulob ɗin bai bayar da cikakkun bayanai kan jimillar kuɗin da suke biyan kocinsu ba, tsawon shekaru huɗu, wanda hakan ke nuna zargin biyan koci kuɗi a ɓoye sama da yadda suka bayyana a hukumance.

Ana zargin Man City da tuhuma 54 na gaza bayar da cikakkun bayanan kuɗi a kakar wasa ta 2009-10 har zuwa 2017-18. Akwai kuma zargin City da gaza bayar da dadaitattun bayanai game da 'yan wasa da koci a karo 14, daga 2009-10 zuwa 2017-18.

Sannan akwai tuhuma 5 da suka danganci rashin biyayya ga dokokin UEFA ciki har da Adalcin Hada-hadar Kuɗi daga 2013-14 zuwa 2017-18. Akwai ƙarin tuhuma 7 na karya dokar cin riba ta hukumar Firimiya, daga 2015-16 har zuwa 2017-18.

Sauran zarge-zarge 35 sun danganci gazawa wajen ba da haɗin-kai ga binciken hukumar Firimiya daga Dasamban 2018 har zuwa Fabrairun 2023.

Ba a sa ran yanke hukunci kan shari'ar har sai farkon baɗi, saboda ɗaukaka ƙara da da idan aka yi zai tsawaita lokacin shari'ar har zuwa 2025.

A kwantar da hankali

Ganin yadda shari'ar ta fara ta da ƙura, hukomomin ƙungiyar Man City sun gaya wa 'yan wasansu da su 'kwnatra da hankalinsu', inda suka tabbatar musu da cewa kulo ɗin ba saɓa ɗaya cikin zarge-zargen 115 da aka masa ba.

Barazanar dakatarwa daga buga gasar Firimiya ɗungurungun, za ta iya karya lagon zaratan 'yan wasan da ke buga wa Man City wasa a halin yanzu, da ma masu burin zuwa ƙungiyar.

Manchester City ce ke riƙe da kofin Firimiya, bayan da ta kafa tarihin lashe kofin sau huɗu a jere, baya ga cewa sun lashe kofin Zakarun Turai a bara, ƙarƙashin koci Pep Guardiola.

TRT Afrika